✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin tumatur din dangote ya fara aiki a Kano

Kamfanin sarrafa tumatur na Dangote wato dangote Tomato Processing Company ya fara aiki, inda a shekaranjiya Laraba ya fara sayen kaya daga hannun manoma da…

Kamfanin sarrafa tumatur na Dangote wato dangote Tomato Processing Company ya fara aiki, inda a shekaranjiya Laraba ya fara sayen kaya daga hannun manoma da wasu manyan dillalai na kayan gwari domin fara sarrafawa.
Aminiya ta ziyarci sabon kamfanin don ganin yadda ake hada-hadar sayen kaya da  shigar da kayan zuwa cikin kamfani wajen auna su kan sikeli domin  tabbatar da cewa kowane mai kaya an tantance yawan kayansa bisa  ma’aunin kilo, lamarin da masu kai kayan suka nuna gamsuwarsu bisa yadda aka fara gudanar da harkar sayen kayan sarrafawa a wannan kamfani.
An yi wani tsari, inda aka samar da guraren yin rumfa domin tara kaya kafin daukar su zuwa cikin kamfanin wajen awo, sannan mafiya wani mutum da wakilinmu ya zanta da shi ya bayyana cewa da “yardar Allah wannan kamfani zai wadatu da kayan sarrafawa da yake bukata musamman ganin cewa Allah Ya albarkaci Jihar Kano da sauran jihohi makwabta da  tumatur mai matukar kyau.”
Alhaji Usman dan Gwari, jigo ne a  sana’ar noman tumatur da kuma  dillancinsa, ya shaidawa wakilinmu cewa suna matukar godiya ga Alhaji Aliko dangote saboda kishin da ya nuna na kafa wannan kamfani na sarrafa tumatur a Jihar Kano bisa  la’akari da yadda ake nomansa a fadin jihar.
Har ila yau, ya  jaddada cewa za su yi kokarin  ganin cewa  kamfanin yana samun kason kayan da yake bukata daga garesu.