✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin sarrafa leda na taimaka wa mata da matasa wajen sana’a

Kamfanin Sarrafa Tsofaffin Leda na Bauchi (Waste Recycling) ya fara aiki kimanin shekara daya da watanni domin sayen ledodin da aka watsar a sassan jihar…

Kamfanin Sarrafa Tsofaffin Leda na Bauchi (Waste Recycling) ya fara aiki kimanin shekara daya da watanni domin sayen ledodin da aka watsar a sassan jihar daga jama’a da ke bin bola suke tsintowa don kai wa kamfanin, a gyara a sake sarrafa su a sayar a wasu kamfanonin da suke yin kayan aikin yau da kullum na roba. Don haka wakilinmu a Bauchi ya tattauna da Manajan kamfanin, Alhaji Yusuf Jibrin Barka. Ga yadda hirar ta kasance game da ayyukansu:

Manaja Yusuf Barka a gefen injinan sarrafa leda

Aminiya: Yaya aikin wannan kamfani ke gudana a halin yanzu?
Yusuf Barka: Aikin wannan kamfani na sarrafa leda a Jihar Bauchi yana tafiya cikin nasara. Muna sayen leda a wajen mata da matasa a kan kowane kilo Naira 30, kuma muna da wakilan da suke saye daga hannun jama’a a kowace karamar hukuma, idan su ne suka kawo mana, sai mu saya a kan Naira 35 kilo, saboda kudin da suka kashe na kawo kayan suna da Naira biyar kan kilo. Muna sarrafa ledar tun daga zabar wadda ta dace mu jefa a cikin injin, sai ta wuce a gutsutsura ta, sai ta shiga wani waje mai ruwa ya wanke ta. Daga nan sai ta wuce inda iska za ta hura domin danshin jikin ledar ya ragu, daga nan sai wani inji ya murtsika ta, sannan ta wuce inda zafi zai narkar da ita, ta fita kamar taliya, ta shiga cikin ruwa ta zama gudaji, ta fito a bushe bayan injin ya yayyanka ta ta koma kanana. Daga can sai mu zuba a cikin buhu a dinke a ajiye don sayar wa sauran kamfanoni masu sarrafa wa. Ana kuma yin tamfol na rufe kaya da butoci da bokatan roba da tabarma da sauran kayayyakin da ake yi na roba. Ledar kuma ta kasu kashi biyu, akwai mai laushi da mai tauri wato irin ta ruwan sha da wacce ake zuba kaya wato mai nauyi, duk hanyar sarrafawa daban-daban ne.
Aminiya: Yaya batun riba da kuma samun kasuwar masu sayen wannan leda?
Yusuf Barka: Malam Isa Yuguda ya kafa wannan kamfani ne domin wadanda ba su da aikin yi na dogaro da kai, idan mutum bas hi da girman kai ko kasala, zai bi duk inda leda take ya tsince idan ya samu kamar kilo 15, yana da Naira dari biyar ke nan. Ka ga duk wanda ba shi da abin yi, aiki ya samu a sauki. Hatta yara idan sun dawo makaranta za su tsinto su kai gida su tara sai a kawo mana mu saya, ta nan an samu abin ba yara kudin tara, nauyi ya ragu ga mazaje, taro sisi zai shiga hannun mata da yara. Bayan haka ga tsabtace muhalli, ledar da ke cike magudanun ruwa za ta ragu haka ingancin kasa da leda ke ragewa zai ragu. Wannan alheri ne ga mutanen Bauchi. Tun shekarar 2008 aka sayo injinan guda uku aka kafa daya, saura biyun za a kafa su nan ba da jimawa ba, don aiki ya inganta.
Aminiya: Kuna samun kudin sayen leda, kuma kamar ta nawa kuke saye a wata?
Yusuf Barka: Alhamdulillahi, tun daga kafa wannnan ma’aikata a watan Yunin 2012 kudi ba ya yanke mana, saboda an dora muhimmancin mutane su samu abin yi da wannan dama. A kowane wata muna sayen leda ta kusan Naira miliyan guda. Da muka fadada zuwa kananan hukumomi, mun nemi karin kudi don kada a kawo leda mu ce ba mu da kudin saye, kowa ya kawo muna saya. Kuma muna jan hankalin masu kawowa su rika gyara ta kafin a kawo. An kafa wannan waje ne domin kishi ba don riba ba. Muna samun wasu masu gauraya duwatsu a tsakiyar buhun da aka zuba ledar ko kuma a daura kasa leda guda ko ruwa don ya ja kilo. Hakan ya sa muke wargaza buhu mu duba kafin dorawa a sikeli. Matsalolin da muke fiskanta da abokan hulda ke nan.
Aminiya: Yaya yanayin kasuwa da masu saye daga wajenku?
Yusuf Barka: Dalilin kafa wannan kamfani shi ne taimakon mutane, ba domin kasuwanci ba. Kuma muna fuskantar rashin wuta da janareta muke aiki, wanda ke shan mai, kuma ana kawo ledar da datti da ha’inci kala-kala, sabanin a Legas da sai mutum ya wanke ya kai a saya, mu kuma nan ba wadatar ruwa, don kar mu kashe guiwar mutane muke saye ko yaya. Yawanci kuma idan mun saya, muna zubar da fiye da rabi kafin mu gyara, don haka babu riba tattare da wannan kasuwanci, sai ko a nemi mayar da kudi don taimakon mutane su samu abin yi, kuma shi ya sa gwamnati, har yanzu take biyan ma’aikata. Muna da ma’aikata tara da ke jikin inji; masu shara bakwai; masu gadi da masu lura da janareta da rijiyar burtsatse, sun kai 30 a waje kuma ga masu tattara leda da diloli masu sayen leda a cikin Bauchi da wajenta. Muna da mutane masu yawa. Kuma muna la’akari da ribar mutum, ba za mu bari ya fadi ba.
Aminiya: Ko kuna da wani shirin hada guiwa da kamfanin sarrafa robobi mallakar gwamnatin Jihar Bauchi?
Yusuf Barka: Tun lokacin da aka bude wannan waje, an nemi a hada wannan kamfani da na roba da kuma na kayan karau (ceramic) da ke Misau don su yi aiki tare. Don haka nake kiran jama’a su sadaukar da kai wajen inganta harkokinsu da mu, ta tsabtace ledar da ake kawo mana, don injinanmu su zama masu inganci, saboda idan injinan suka hadu da kasa muna samun matsala sosai.