Kamfanin Mouka, ja-gaba a harkar katifu da matasan kai da sauran kayayyakin kwanciya a Najeriya, ya kaddamar da sabon gangamin karfafa gwiwar ’yan Najeriya su ba da muhammaci ga samun lafiyayyen barci domin samun rayuwa mai inganci.
Shugabar Kungiyar Kula da Lafiyar Jiki ta Najeriya (NSP), a Jihar Legas, Dokta Remilekun Durojaiye, ta bayyana barci da abinci da motsa jiki da kuma rage damuwa a matsayin ginshikan samun ingantacciyar rayuwa.
Dokta ta Remilekun Durojaiye ta ce abubuwa uku da ’yan Najeriya za su kiyaye don samun rayuwa mai inganci su ne motsa jiki na akalla mintoci 150 a duk mako; cin lafiyayyen abinci hade da ’ya’yan itatuwa da kayan marmari da kuma shan ruwa mai yawa; sai na uku, kwanciya a bisa katifu da matashin kai masu inganci irin na Mouka.
Ta ce, “samun lafiyayyen barci na kara lafiyar jiki da kuma walwala,” sannan bincike ya tabbatar da cewa barci na kara garkuwar jiki, domin mutanen da ba sa samun isasshe ko lafiyayyen barci suna iya kamuwa da rashin lafiya, bayan kamuwa da kwayar cuta.
Haka zalika barci na kara wa zuciya lafiya sannan rashin samun barci na akalla sa’o’i bakwai a kowane dare na kara hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da na hawan jini.
Bincike ya gano cewa akwai alaka mai karfi tsakanin rashin barci da hadarin kamuwa da ciwon sukari nau’i na 2.
Wani amfanin na barci shi ne debe gajiya da kara karsashin yin aiki.
Dokta Remilekun ta kuma yi gargadi ga ’yan Najeriya cewa “illolin rashin barci na gajeren zango sun hada da rashin nutsuwa, mantuwa, damuwa da kuma kasala.
“Illolinsa masu dogon zango kuma su ne raguwar nagartar aiki, karancin fahimta da kuma karuwar hadarin samun tabin hankali.”
Da yake bayani kan gangamin wayar da kan, Babban Manajan Samar da Samfura na Kamfanonin Mouka, Akeem Audu, ya ce “A matsayinmu na masu samar da kayan kwanciya a Najeriya, hakkinmu ne ilmantar da masu amfani da kayayyakin da muke samarwa.
“Takenmu shi ne karo jin dadin rayuwa ta hanyar samar da kayan kwanciya masu nagarta tare da tabbatar da cewa kwastomominmu sun rungumi dabi’ar samun lafiyayyen barci.
“Samun walwalar ’yan Najeriya shi ne abin da muka sa a gaba,” in ji shi.
Mouka wani bangaren ne na Rukunin Kamfanin Dolidol International mai hedikwata a kasar Maroko, da ke samar da samfura daba-daban masu inganci na katifun marasa lafiya, matasan alfarma, har da katifun yau da kullum da aka samar ta fasahar musamman ta Bio-Crystal.
Kayayyakin Mouka sun samu amincewar Kungiyar Kula da Lafiyar Jiki ta Najeriya (NSP) sun dace da ka’idojin kungiyar.