A shekaranjiya Laraba ce Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya karrama wadansu daga cikin ma’aikatansa 25.
Karramar wadda kashi hudu ce: Akwai wadanda aka karramar kan Gaskiya da Rikon Amana da aka ba Mataimakiyar Editan Daily Trust Sunday, Stella Iyaji da Sakinat Mustapha Motunyaro daga ofishin Legas, sai wadanda aka karrama kan Aikin Tukuru kwarewa da aka ba mai tsara shafuka, Stanley Bainta da Sunday Michael Echewofu. Kuma an karrama wadanda suka kai shekara 10 ko 15 suna aiki da kamfanin.
Daga cikin wadanda suka kai shekara 15 a kamfanin su 7, akwai tsohon wakilin Aminiya, yanzu Mataimakin Manaja, Harkokin Kasuwanci da Tallace-Tallace na Jaridar Aminiya Malam Abubakar Haruna da Ruby Aledander Leo da Maimuna Sani da sauransu.
A bangaren wadanda suka yi shekara 10 suna aiki da kamfanin su 14 kuwa, akwai Mukaddashin Editan Aminiya, Malam Salihu Makera da Hajiya Lubabatu I. Garba wakiliyar Aminiya a Jihar Kano da Umoru Faruk Salifu da sauransu.
Da yake jawabi a wajen bikin karramar, Babban Jami’in Zartarwa kuma Babban Editan Kamfanin, Malam Mannir dan-Ali, ya ce ana shirya bikin ne domin a karrama ma’aikata masu gaskiya da rikon amana da masu kokari wajen aiki da kuma wadanda suke da hakuri da juriya wajen kasancewa tare da kamfanin na tsawon lokaci. Sai ya bayyana wadanda aka karrama da cewa, “Ba don ku ba, da kamfanin bai kai inda yake a yanzu ba.”
Bikin karramawar, wanda aka yi a otel din Chida da ke Abuja, ya samu halartar dukan daraktoci da shugabannin kamfanin da kuma dimbin ma’aikata daga sassan kasar nan.