Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa Maso Yamma a Majalisar Dattawa, Sanata Babangida Husaini ya bayyana damuwarsa kan tashin farashin kayan abinci musamman a lokacin girbi.
Sanatan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya raba wa ’yan jarida.
- NAF ta hallaka ’yan ta’adda sama da 70 a Borno
- Dalilin da ke hana ci gaban noma a Nijeriya — Suleiman
“Na lura cewa farashin kayan abinci yana ƙaruwa ta fuska da dama a faɗin yankunan karkara a jihohin Arewa da sauran sassan ƙasar nan,” in ji shi
“Wannan yanayin da kuma nauyin da ya shafi tattalin arziƙi a kan jama’a yana da ban tsoro, musamman a farkon lokacin girbi lokacin da ake sa ran sayar da kayan abinci a kan farashi mai rahusa.
“Babban abin takaici shi ne rashin tsaro da ‘yan fashi da sauran munanan ayyuka na masu aikata laifuka a mafi yawan yankunan da ake noman abinci.”
“Sauran matsalolin su ne suka haifar da hauhawar farashin abinci da ƙarancin abinci a cikin al’umma,” a cewarsa.
Har ila yau, Sanatan ya ƙara da cewa “Wannan mummunan yanayi na buƙatar a ɗaukar matakin gaggawa kafin abubuwa su ƙara faskara domin hakan na nuni da babbar barazana ga tsaron abinci da zaman lafiyar ƙasarmu.”
A gefe guda, ya yi kira ga Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi, da masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakai domin daƙile barazanar.
Hakazalika, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu domin ya samo bakin zaren bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan.