✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin jiragen Emirates zai ci gaba da aiki a Najeriya

Ya janye dakatar da harkokinsa a Najeriya kan rikicin kudi

Sati guda bayan rufe harkokinsa a Najeriya, Kamfanin Jiragen Sama na Hadaddiyar Daular Larabawa (Emirates) ya  ce zai dawo aiki kasar  ranar 11 ga watan Satumba.

Emirates ya sanar da sabon matakin ne bayan Babban  Bankin Najeriya (CBN) na sahale biyan sa Dala 256m domin rage kudadensa da ke hannun gwamnatin Najeriya.

Kafin sanar rufe harkokinsa, da farko Emirates ya rage yawan zirga-zirgar jiragensa a Najeriya, daga sahu 11 zuwa bakwai.

Daga bisani ya rufe dukkanin hanyoyin siyar da tikitinsa ta intanet, domin fara aiwatar da daina aiki daga ranar Alhamis.

To sai dai shiga tsakanin da CBN din ya yi, ya sanya jiragen kasashen ketare da dama na waje irinsu British Airways, ajiye aniyarsu ta daina aiki a Najeriya, kamar yadda Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya ta bayyana.

Sai dai, Emirates ya ce zai ci gaba da aiki ne amma ba kamar yadda ya saba yi kafin aukuwar lamarin ba.

A ranar 11 ga watan Satumba dai kamfanin zai dawo aiki a Legas, inda zai rika yin sawu hudu duk mako, har sai gwamnatin Najeriya ta cika masa ragowar bashin da yake bi.