Kamfanin nan da ya ƙwace jiragen saman Fadar Shugaban Kasan Najeriya guda uku a ƙasar Faransa, ya sake ƙwace wani jirgin ƙasar a Kanada.
Kamfanin Zhongshang Fucheng Industrial Investment Ltd, ya ƙwace jiragen Najeriya da wasu kadarorinta a wasu ƙasashe ne sakamakon rikicin da ke tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Ogun.
A kwanakin baya ne Zhongshang Fucheng ya ƙwace jiragen Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya a Faransa bayan wata kotu da ke can ta ba shi nasara bayan sauraron ƙarar da ya shigar kan lamarin.
Daga baya Zhongshang Fucheng ya saki ɗaya daga cikin jiragen fadar shugaban ƙasan Najeriyan a matsayin abin da ya kira ƙarimci, sakamakon ganawar da aka shirya tsakanin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron.
- ’Yan bindiga na neman N50m kan mutane 10 da suka sace a Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Gudummuwar ‘Yan Najeriya Wajen Cin Hanci Da Rashawa
A ranar Litinin Tinubu ya yi bulaguro zuwa Faransa a ɗaya daga cikin jiragen, samfurin Airbus A330, a yayin da ake tsaka da dambarwa kan sayen sa, bayan kamfanin ya sake shi.
A kwanan kuma Zhongshang Fucheng ya samu sahalewar wata kotu na karɓar takardun mallakar wani ƙarin jirgin Najeriya ƙirar Bombardier 6000 daga hukumomin ƙasar Kanada.
Wata kotu ce da ke zamanta a Quebec ce ta ba Zhongshang izinin ƙwace jirgin daga hannun Najeriya bayar sauraron shari’ar da kamfanin ke neman diyyar Dala miliyan 70 daga gwamnatin Najeriya.
Zhongshang ya ƙwace kadarorin Najeriya da dama a ƙasashen waje, baya ga jiragen sama da suka haɗa da Dassault Falcon 7X a birin Paris na ƙasar Faransa; Boeing 737; Airbus A330 da kuɗin ya kai Dala miliyan 100; sai kuma Bombardier 6000 da yanzu kamfanin ya ƙwace a ƙasar Kanada.
A watan Maris 2024 ne Mai Shari’a David Collier na Babbar Kotun Quebec ya yi watsi da roƙon gwamnatin Najeriya na ci gaba da mallakar Bombardier 6000 din.
Bayanai sun nuna cewa wani gudajjen mai laifi, Dan Etete, ne ya sayi jirgin a kan Dala miliyan 57, daga cikin Dala miliyan 350 da ya samu a badaƙalar sayar da rijiyar mai mai lamba OPL 245 a shekarar 2010.