✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin BUA ya ba UNIMAID tallafin N1bn

Tallafin na daga cikin tsare-tsaren kungiyar ASR na habaka Jami'o'i a Najeriya.

Fitaccen dan kasuwa kuma shugaban kamfanin BUA, AbdulSamad Rabiu, ya ba da tallafin Naira biliyan daya ga Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), don sabunta ta.

Sanarwa da Mataimakin Daraktan Yada Labaran UNIMAID, Mohammwd T. Ahmed ya fitar ta ce an bayar da tallafin ne ta hannun Kungiyar AbdulSamad Rabiu (ASR).

Daraktan Kamfanin BUA, Dokta Idi Hong ne ya bayar da tallafin yayin wata ziyara da kungiyar ASR ta kai wa Shugaban Jami’ar, Farfesa Aliyu Shugaba.

Hong ya ce tallafin na daga cikin tsare-tsaren kungiyar ASR na tallafa wa jami’o’i wajen bunkasa su da samar musu da cigaba.

Dokta Hong, ya ce a duk shekara ASR na fitar da Dala miliyan 100 don ba tallafa wa harkar ilimi, lafiya da cigaba al’umma, wanda daga ciki ake ware wa Najeriya Dala miliyan 50, ragowar kuma ake ba wa sauran kasashen Afrika.

ASR ta ba da irin wannan tallafi ga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Jami’ar Ibadan, Jami’ar Benin da kuma Jami’ar Ilorin.

Da yake nasa jawabin, Farfesa Shugaba, ya ce UNIMAID za ta yi amfani da tallafin ta hanyar da ta dace wajen samar da sana’o’i’n dogaro da kai da kuma bunkasa abubuwan rayuwar al’umma.

Sannan ya ce za su tabbatar da sun horar da dalibai kan muhimmancin dogara da kai, tare sa rage wa gwamnati tarin aikin da ke kanta.