✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Boulos ya yi wa dillalansa albishir

Kamfanin Boulos Enterprises Limited da ya kware wajen hada injinan motoci da babura tare da hadin gwiwar kamfanin kera mota na Suzuki da ke kasar…

Kamfanin Boulos Enterprises Limited da ya kware wajen hada injinan motoci da babura tare da hadin gwiwar kamfanin kera mota na Suzuki da ke kasar Japan, ya jaddada kudirinsa na ci gaba da samar wa abokan huldarsa injina wadanda za su dace da yanayin muhalli na kasar nan.

Shugaban kamfanin Boulos Robert N. Ugbaja shi ne ya yi furucin yayin da yake gabatar da jawabin maraba ga dillalai a taron da kamfanin ya yi da dillalansa a dakin baje kolin kayayyakin kamfanin a Legas a Larabar da ta gabata.
Ya ce “kudirin da muka dauka na hada karfi da karfe da kamfanin Suzuki na kasar Japan don biyan bukatun abokan huldarmu shi ya sanya muka ci gaba da kawo sabbabin injina iri-iri.
Shi kuwa Janar manaja na kamfanin, Julian Hardy, ya baiwa dillalan kamfanin tabbacin ci gaba da biyan bukatunsu. Ya bayyana cewa kamfanin Boulos ya yi kyakkyawan tanadi ga abokanen huldarsa da suka sayi inji mai salo hudu na tallafin gyara da kuma samar musu da kayan gyara.
Dillalan kamfanin da dama da Aminiya tattauna da su sun bayyana farin cikinsu ga sabon injin ‘Four Stroke’ da kamfanin ya bullo da shi. Sun yaba wa kamafanin da ya samar da kayan gyara da tare da wayar musu da kai dangane da harkokin kamfanin.