✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Azman Air ya goyi bayan wasan kwallon kafar MATCH4IDPS

Kamfanin Zirga-zirgar jragen sama na Azman Air ya bayyana aniyarsa na goya wa wasan kwallon kafar da za a yi don ’yan gudun hijira da…

Kamfanin Zirga-zirgar jragen sama na Azman Air ya bayyana aniyarsa na goya wa wasan kwallon kafar da za a yi don ’yan gudun hijira da ke fadin kasar nan, wanda za a yi tsakanin ‘yan kwallon Kano Pillars da kuma manyan ‘yan wasan African Legends, wasan da aka yi wa take da MATCH4IDPS wanda za a yi a jibi ranar 14 ga watan Disambar 2017.

Babban Daraktan Kamfanin Azman Air Alhaji Faidal Abdulmunafi ya bayyana cewa a shirye kamfaninsu yake ya shiga a dama da shi cikin irin wadannan ayyuka da ake yi don tausaya wa tare da taimaka wa ’yan gudun hijira a fadin kasar nan. “Muna farin cikin kasancewa daya daga cikin wadanda za su marawa wannan biki mai dimbin tarihi baya.

Kasancewar  za a gudanar da wannan wasan a Jihar Kano, don haka bikin  da ba wai kawai inganta rayuwar wasu mutane kadai zai yi ba, a waje daya kuma zai zama ya kara daga suna da darajarar Jihar Kano a idon duniya.

A cewar babban daraktan kamfanin na Azman Air wasan zai zama wata kafa da za ta kara bunkasa harkokin kasuwanci a Jihar Kano. “Wannan wasa a wurinmu abin alfahari ne domin zai zama wata hanya da za ta ba ’yan

kasuwa damar baje-kolin hajojinsu sannan kuma ta kara bunkasa Jihar Kano da al’adunta a idon duniya.”

Alhaji Abdulmunafi ya yi kira ga sauran ’yan kasuwa a Jihar Kano da sauran sassan kasar nan da su ba wannan wasa wanda za a yi domin ’yan gudun hijira goyon baya ta yadda za a samu nasarar wasan kamar yadda

ake fata.

Ita ma a nata jawabin Kodinetan shirya wasan, Madam Abi Goodman ta bayyana cewa ’yan wasan Afrika da suka hada da Elhadji Diouf da Nwankwo Kanu da Mutiu Adepoju da Mohammed Kalon da Luka Sodobe da Febian

Mukati za su taka leda a wasan inda za su kara da ’yan wasan Kano Pillars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.