✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Apple zai kalubalanci kotun Amurka

Kamfanin Apple ya ce zai kalubalanci wata kotu da ke Jihar California ta kasar Amurka, wacce ta bayar da umarni a yi kutse cikin wayar…

Kamfanin Apple ya ce zai kalubalanci wata kotu da ke Jihar California ta kasar Amurka, wacce ta bayar da umarni a yi kutse cikin wayar daya daga cikin mutanen da suka kai hare-haren garin San Bernadino wacce ke kulle da nufin taimaka wa hukumomi a binciken da suke gudanarwa.
A wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Kamfanin  Tim Cook, ya ce idan har ana so ya yi biyayya ga umarnin kotun, to wajibi ne Apple ya samar da wata manhaja wacce za ta iya bude duk wayoyin da kamfanin ya kera.
Ya yi gargadin cewa hakan zai yi barazana ga sirrin masu mu’amala da wayoyin na Apple, kamar yadda BBC ta bayyana.
Syed Rizwan Farook da matarsa sun kashe mutum 14, kana suka jikkata mutum 22 a harin da suka kai a watan Disambar da ya wuce.