daya daga cikin memba a Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) a ranar Litinin da ta wuce ne ya bayyanawa manema labarai cewa kamfanin da ke samar da kayayyakin wasanni ga Najeriya mai suna Adidas ya daina hulda da kasar don haka daga yanzu sai dai kasar ta nemi wani kamfanin amma ba shi ba.
Kodayake an samu rahoton da ya nuna mai magana da yawun hukumar ta NFF Ademola Olajire tuni ya fara tattaunawa da wadansu kamfanonin da ke samar da kayayyakin wasanni don maye gurbin kamfanin na Adidas nan ba da dadewa ba. A wata hira da kafar sadarwar sashen wasanni na BCC ta yi da shi, Olajire ya tabbatar da wannan labari kuma ya ce akwai yiwuwar Hukumar ta shawo kan kamfanin Adidas don ya canza ra’ayi a kan matakin da ya dauka na daina hulda da kasar nan.
Sai dai rahotanni sun nuna da wuya kasar ta samu wani kamfanin da zai maye gurbin na Adidas a wannan lokaci musamman gannin yadda ake samun yawan dambarwar shugabanci a Hukumar ta NFF da kuma yadda kasar ta kasa kai batenta na halartar gasar cin kofin Afirka da zai gudana a watan Janairun badi a Ekuitorial Guinea idan Allah Ya kaimu.
Sai dai mai magana da yawun Hukumar ta NFF Ademola Olajire ya ce idan har ba su samu wani kamfanin da zai dauki nauyin samar da kayayyakin wasanni ga Najeriya ba, to ba su da wani zabi illa su karkata akalarsu zuwa kasar Sin watau China don neman kamfanin da zai cigaba da daukar nauyin samar musu da kayayyakin wasanni.
“Idan Najeriya ba ta samu kamfanin da zai dauki nauyin samar da kayayyakin wasani daga nan zuwa watanni uku masu zuwa ba, ko shakka babu hukumar za ta shiga matsala a wajen samar da kayayyakin wasanni kuma hakan ba karamar cikas ba ne”, inji shi.
Shi dai kamfanin Adidas tun a watan Agusta ne ya rubuta takardar koke ga Hukumar NFF a kan yadda kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi tare da wadansu daga cikin ’yan kwallonsa suke amfani da rigar wasanni ta wadansu kamfanoni daban da na Adidas duk kuwa da kwantaragin Dala miliyan 7 kwatankwacin Naira biliyan 1 da dubu dari 1 da kamfanin ya kulla da Najeriya a tsawon shekara daya. Don haka yanzu da wa’adin kwamtaragin ya kare ne sai kamfanin Adidas ya yanke shawarar daina hulda da Najeriya.
Sai dai masana harkar kwallo suna ganin babban dalilin da ya sa kamfanin ya daina yin hulda da NFF shi ne ganin yadda kasar take samun koma-baya a harkar kwallo.
Kamfanin Adidas ya daina hulda da Najeriya
daya daga cikin memba a Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) a ranar Litinin da ta wuce ne ya bayyanawa manema labarai cewa kamfanin…
