✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfani ya kirkiro na’urar adana kayan miya su yi wata 3 ba su lalace ba

Kamfani ya kirkiro sundukin adana kayan miya su yi wata 3 ba su lalace ba

Wani kamfani a Zariyan Jihar Kaduna ya kirkiro wani sunduki da zai iya adana kayan miya da sauran kayan lambu har su yi wata uku ba su lalace ba.

Kamfanin mai suna ColdHub da haɗin gwiwar Heifer International ne ya samar wa manoma sabuwar fasahar da nufin a rage asarar kayan da suke nomawa, musamman tumatir.

An gabatar da sundukin ne yayin bikin bude cibiyar sanyaya kayan lambu a wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a harabar kasuwar Dan Magaji da ke Zariyan.

Kungiyoyin manoma masu noma kayan marmari da ‘yan kasuwa da kuma sarakunan yankin da dama ne dai suka suka sami halartar taron.

Cibiyar na kuma kunshe da kayan zamani da za su rika sanyaya amfanin gona na kayan gwari kamar su tumatir da kabeji da albasa da sauran kayan noma.

Kazalika, ana iya adana abubuwa kamar su kifi da nama har da madara, wanda yakan kai kusan wata uku ba su lalace ba.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban kamfanin na ColdHub, Nneameka Ikegwuonu, ya ce an samar da shi shirin wasu jihohin Arewaci da Kudancin Najeriya, kuma mutane na amfani da shi saboda yana taimakawa don adana abubuwan da ake nomawa a Najeriya.

A cewar shi, manufar samar da tsarin a Zariya shi ne saboda gari ne da yake da dimbin manoma da suke noma kayan gwari, kuma ana samun koma-baya a lokuta da yawa saboda rashin samun kulawar da ta dace.

Ya godewa al’ummar yankin saboda ba su hadin kai da goyon baya cikin shirye-shiryensu.

Da yake nashi jawabin, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, wanda Sarkin Yakin Zazzau, Alhaji Yahaya Fate ya wakilta, ya yaba wa kokarin kamfanin na samar da matsugunisa a Zariya wadda manoma da dama za su amfana.

Wasu daga cikin manoman da suka halarci taron sun nuna farin cikinsu na samar da wannan tsari, kuma suka yi fatan zai kara taimaka wa kayan da suke nomawa da rani da kuma damina.