A yayin da kasashen duniya ke nesa-nesa da Rasha, kasar Kamaru kulla yarjejeniyar aikin soji da ita.
Bayanai sun bayyana cewa ministocin tsaron kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a satin da ya gabata a birnin Moscow na kasar Rasha.
- Hatsarin jirgin sama 11 da suka kashe hafsoshin sojin Najeriya
- DAGA LARABA: Kokarin Da Gwamnati Ke Yi A Yakar ’Yan Ta’adda
Yarjejeniyar dai na kunshe ne a cikin wani daftari mai shafi 13, inda ministan tsaro Joseph Beti Assoma na Kamaru ya sanya wa hannu a madadin kasarsa, yayin da takwaransa na Rasha, Janar Sergei Choigou ya sanya hannun a madadin kasar Rasha.
A sashe na biyu na yarjejeniyar, kasashen biyu sun amince da yin musayar bayanan sirri da suka shafi siyasar kariya da kuma tsaro a tsakaninsu.
Kazalika, za su kuma rika bayar da horon aikin soji, horas da sojoji a fannin kiwon lafiya da kuma kara gogewa a kan taswirar kasa.
Yarjejeniyar ya tanadi musayar fasaha tsakanin rundunonin tsaron kasashen biyu, sai kuma tallafa wa juna a duk lokacin da dakarun kasashen biyu suka samu kansu, karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta Majalsar Dinkin Duniya.
Kamaru dai ta kulla wannan yarjejeniya ne da Rasha a lokacin da ake tsaka da janye mu’amala da kasar kan mamayar Ukraine, wanda hakan ya sanya kasashe da dama sanya mata takunkumi.