✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamanta gaskiya da adalci da rikon amana suka kai Daily Trust inda yake a yau

A ranar Alhamis din makon jiya aka yi bikin cika shekara 20 da kafa kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya da sauransu, tare da…

A ranar Alhamis din makon jiya aka yi bikin cika shekara 20 da kafa kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya da sauransu, tare da wani taron tattaunawa inda masana harkokin watsa labarai suka yi waiwaye da fashin baki kan nasarori da kalubalen da ke fusakantar aikin jarida a kasar nan. Taron da tsohon Shugaban Kamfanin Buga Jaridun Punch Cif Ajibola Ogunsola ya shugabanta, mai taken: “Aikin Jarida A Matsayin Kasuwanci: Labarai ,Ra’ayoyi da Tallace-Tallace,”  mahalartarsa sun yi tsokaci kan wadannan batutuwa a kan jaridun wannan kasa. 

Ko shakka babu, Kamfanin Daily Trust ya cancanci ya yi wancan biki kasancewar wasu kamfanonin ma bikin cika shekara daya suke yi, ballantana inda aka cika shekara 20, kullum gaba ake yi. Kamar yadda Shugaban Kamfanin, kuma Babban Editan Jaridun na farko Malam Kabiru Yusuf ya fada a wata ganawa da ya yi da manyan editocin kamfanin don share fagen bikin cewa a daki daya suka fara buga jaridar ta Daily Trust lokacin tana Weekly Trust (mai fitowa a ranar Juma’a) a ranar 24-03-1998, a Kaduna. Na samu labari cewa bayan cika shekara daya da kafa kamfanin, Malam Kabiru Yusuf, ya zauna ya yi lissafi inda ya gane cewa a tafiyar da suka ratso ta shekara daya, ba yabo ba fallasa bisa ga abin da suka zuba na jari, wato ma’ana ba su ci riba ba bare a ce an fadi.

Hakan ya ba shi kwarin gwiwar ya ci gaba a kan abin da ya sa gaba. Don haka a watan Janairun 2001 suka fara buga jaridar kullum-kullum da sunan Daily Trust, sai ta ranar Lahadi wato Sunday Trust da ta biyo baya a shekarar 2006, sai wannan jarida ta Aminiya da kamfanin ya haifa a shekarar 2006. A shekarar 2015, Kamfanin ya fara buga jaridar kananan yara mai suna Teen Trust sai ta harkokin wasannni mai suna Trust Sport da aka fara buga wa kwanan nan. Akwai mujalla mai tsokaci a kan al’adun Afirka mai suna Kilmanjaro da ta mata, wato Tambari da sauransu. Malam Kabiru ya fadi cewa ba shakka sun fara buga jaridar da kafar dama, domin kuwa a fadarsa duk da karancin kudi da sauran kalubale na yau da kullum da suke fama da su, musamman tsadar rayuwa da ta samo asali daga faduwar darajar tattalin arzikin kasar nan da ta jawo masu hauhawar farashin kayyayyakin dab’i da karancin wutar lantarki da tsadar man gas da dawainiyar raba jarida, su a cikin yardar Allah sun samu karbuwa a gida da waje.

Wannan nasara kuma bayan katafaren hedkwatar kamfanin da ke Abuja, suna da ofisoshin yanki a biranen Legas da Kano da Maiduguri inda a can suke buga jaridun kullum, yayin da suke fatan zuwa karshen bana za su bude irin wannan ofishi a Sakkwato birnin Shehu, dukansu mallakin kamfanin Media Trust inji Malam Kabiru Yusuf. Kamar yadda na fadi a sama, lallai akwai bukatar a ce an yi wancan biki kasancewar, kafin da bayan zuwan jaridun Trust akwai jaridu da mujallu daban-daban da ake da su a kasar nan wala’alla mallakin Gwamnatin Tarayya ko na jihohi da na ’yan kasuwa da suka mace ko aka daina jin amonsu sam-sam, irin su jaridun Daily Times da New Nigerian da Sketch da Obserber da Newswatch da Sunray da The Week da Crystal da Reporter da NEdT da Democrat da Standard da Herald da sauransu, amma kamfaninn Media Trust sai dada bunkasa yake yi kullum. 

A tawa ’yar guntuwar fahimtar wannan nasara ba ta rasa nasaba daga sunan da aka rada wa kamfanin da ke dauke da kalmar Trust da a Hausa take nufin aminci (Amana) ko amincewa da irin jagorancin da aka kafa kamfanin a kansa tun farko. Dadin dadawa na san cewa a lokacin Malam Kabiru shi ya bi abokansu na kusa-kusa wadanda ya amince za su iya tafiya tare ya fadakar da su abin da ya sa a gaba da dalilin da zai sanya sub a da kudinsu a zaman jari don kafa jaridar. Ba sai na kawo sunayen mutanen da suka amince a wancan lokaci suka ba Malam Kabiru amanar dukiyarsu da zuciya daya ba, amma dai na san dukansu a lokacin bayan kasancewarsu makusanta juna, kuma akwai amincewar juna a tsakaninsu, kuma a lokacin mutum daya tilo daga cikinsu ne kila ya wuce shekara 50, amma wasunsu ma ko 40, ba su kai ba, kuma ba ka iya kiransu masu kudi, kishi kawai ya sa suka yi haka. 

Bayan kamfanin ya yi karfi, alheri ya samu, daraktocin kamfanin sun fuskanci babbar matsalar da ta nemi ta wargaza kamfanin, amma sai suka yi dabara kafin su bari a yayata halin da suke ciki, suna tsakiyar taron wancan ka-ce-na-ce, sai suka yi wuf suka ba da sanarwar suna fa da matsala a junansu, da ba da tabbacin suna kokarin warware ta. A ganina haduwar da suka yi tun farko kasancewarta ta Allah ce, ita ta taimake su suka samu wancan karfi gwiwar da suka samu gaya wa duniya irin matsalar da suke ciki, maimakon su danne maganar, wadda fitarta ta wani fanni daban da ta kawo musu babbar koma-baya.

Yin haka ba karamin adalci ba ne a junansu. Sannan sai ka dubi irin yadda Malam Kabiru Yusuf kusan ka ce shi kadai ya yi ta kai-gwauro yana kai-mari a farkon kafa jarida yana kaddamar da ita a dukan jihohin Arewa da wasu na Kudu, inda a wasu biranen har taimakon kudi aka rika ba kamfanin. Bayan waccan sadaukarwa, yadda kamfanin ya fara tun daga farko na ganin kowane ma’aikaci da irinmu masu ba da gudunmuwa a mako-mako ba wanda aka taba tauye wa hakkinsa. Mai karatu kamfanin ya kai matsayin da shi ne kan gaba wajen biyan gwagwgwaban albashi da alawus-alawus kuma a kan lokaci ga ma’aikatansa a tsakanin gidajen jaridu da mujallu na kasar nan, a lokacin da wadansu mamallaka gidajen jaridu da mujallun suke alfahari da cewa ka samu shaidar katin kana yi musu aiki ma ya ishe ka ka ci abinci koda ba albashi. Kamfanin na Media Trust shi ne na farko a kasar nan da ya fara fitowa karara wajen yaki da rashawar da ake ba ’yan jarida, ta hanyar buga sanarwa a kai-a kai a jaridunsa yana gargadin duk masu hulda da wakilansa da kada su kuskura su rika ba su wani abu da sunan na-goro da ya zama tamkar wajibi a gudanar da aikin jarida a kasar nan.

Da ’yan wadannan bayanai nake cewa kamanta gaskiya da adalci da rikon amana suka kai Daily Trust inda take a yau. Allah kuma Ya kara nuna mana wasu gwala-gwalan shekaru a kamfanin na Media Trust cikin kwanciyar hankali da karuwar arziki a kamfanin da kasa baki daya.