✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalubalen da ke gaban Zababben Shugaban Kasa Tinubu

Akwai tarin kalubale da Tinubu zai fuskanta bayan zamansa Shugaban Najeriya.

A ranar 1 ga watan Maris ne Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da sakamakon zaben Shugaban Kasa a dakin da ake tattarawa da sanar da sakamakon zaben kai tsaye ta kafafan yada labarai.

Jami’in sanar da zaben shugaban kasar, ya ce sakamakon jihohi 36 da Abuja ya nuna cewa, dan takarar Shugaban Kasa na jami’iyyar APC Bola Tinubu ya lashe zaben da kuri’u miliyan takwas da dubu dari bakwai da casa’in da hudu da dari bakwai da ashirin da shida (8,794,726).

Sai kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya zo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan shida da dubu dari tara da tamanin da hudu da dari biyar da ashirin (6,984,520).

Amma shi kuma dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi, da ya zo na uku ya samu kuri’u miliyan shida da dubu dari da daya da dari biyar da talatin da uku (6,101,533).

Shi kuwa dan takarar jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso da ya zo na hudu, ya samu kuri’a miliyan daya da dubu dari hudu da casa’in da shida da dari shida da tamanin da bakwai (1,496,687).

Ina aka dosa?

Kasancewar Najeriya ita ce mafi girman tattalin arziki kuma mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka – mutum miliyan 214 – duk wani abu da ya faru a Najeriya yana da tasiri a fadin nahiyar.

Masu kada kuri’a sun zabi sabon Shugaban Kasa bayan kwashe shekara takwas karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, sai dai kuwa wanda ya yi nasara akwai wasu manyan kalubale da zai yi fama da su.

Ga dai abubuwan da suka fi damun al’ummar Najeriya:

Hauhawar Farashi

A shekarar da ta gabata – kamar sauran al’ummar duniya – ’yan Najeriya sun fuskanci matsalar hauhuwar farashin kayan abinci saboda rikicin Ukraine.

To amma farashin ya fara tashi ne tun kafin yakin Ukraine, bayan da gwamnati ta rufe iyakokin kasar domin hana shigar da wasu kayayyaki.

An kiyasta cewa an samu tashin farashi a shekara ta 2022 da kimanin kashi 19 cikin dari mafi muni ke nan da aka samu cikin shekara 20.

Garin rogo na daya daga cikin abubuwan da tashin farashin bai shafa ba sosai, to har yanzu iyalai na jin radadin tashin farashin abubuwa kamar tumatir da man girki.

Idan sabon shugaban kasar na son ya taimaka wa mutane kan rage radadin farashin abubuwan bukatu na yau da kullum, to zai fuskanci kalubalen cewa yanzu haka gwamnati na kashe fiye da abin da take samu.

Tallafin Man Fetur 

Ana kashe makudan kudade kan tallafin man fetur, kuma kasar mai arziƙin man fetur ta gaza cin gajiyar tashin farashin mai a duniya kasancewar ba ta iya tace mai na a-zo-a gani a cikin gida, dole ne sai ta sayo tataccen man fetur daga waje.

Masu sharhi na damuwa kan ko kasar za ta iya ci gaba da biyan bashin da ake binta, ganin cewa a wasu lokutan cikin shekarar 2022 kudin ruwa kawai na bashin da ake binta ya fi karfin abin da take samu.

A matsayinta ta daya daga cikin kasashen da suka fi fitar da danyen mai a nahiyar Afirka, Najeriya na dogaro da danyen man ne wajen samun kudaden shiga da kuma kudin kasashen ketare.

Sai dai kasar ta kasa cin gajiyar kudaden da take samu daga danyen man – an sace yawancin kudin, wasu kuma an yi wadaka da su.

Haka nan kuma yawan man da kasar ke hakowa na raguwa a cikin shekara 10 da ta wuce.

A 2022 yawan man da ake fitarwa ya yi kasa fiye da kowa ne lokaci a cikin shekara 30.

An dora mafi yawan laifin a kan satar danyen mai da masu farfasa butun mai. Hakan dori ne a kan shekarun da aka kwashe ba tare da zuba isasshen jari a bangaren ba, wanda hakan ya sa kasar ke komawa baya cikin jerin kasashen Afirka da ke fitar da man fetur a nahiyar Afirka.

Tuni dai Gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana cewa za ta daina biyan tallafin man fetur ya zuwa tsakiyar shekarar nan kamar yadda ta yi tanadi a Kasafin Kudin bana.

Matasa na fama da rashin aiki

Abu na farko da matasan Najeriya suke so shi ne aikin yi.

Yanzu haka kashi uku cikin hudu na al’ummar Najeriya ba su da aiki. A bangaren matasa, sama da rabi na ’yan shekara 15 zuwa 24 suna neman aikin yi.

Tabbas matakan yaki da cutar Coronavirus sun taka rawa, to amma yawan marasa aikin yi a kasar na karuwa tun kafin bullar cutar Coronavirus.

Tattalin Arziki na tafiyar hawainiya

Tattalin arzikin kasar na samun ci-gaba tun 2015, sai dai ba ya bunkasa da sauri ta yadda zai samar da aiki ga duk masu neman aikin.

Ana dora wani bangaren na laifin rashin bunkasa tattalin arziki a kan rashin tsaro, amma masana tattalin arziki na ganin cewar karancin kudaden ketare da rufe iyakokin kasar sun sanyaya wa masu zuba jari gwiwa.

Akwai karancin wadatuwar abubuwan bukatu na yau da kullum wadanda za su iya bunkasa rayuwa da harkar kasuwanci.

Wutar Lantarki

An dade ana suka kan karancin lantarki na kasar, alkaluman Bankin Duniya sun nuna cewa kasa da kashi 55% na al’ummar kasar ne ke samun wutar lantarki.

Matsalar Tsaro

Magance karuwar matsalar tsaro a Najeriya shi ma babban kalubale ne ga sabon shugaban kasar.

Lokacin da aka zabi Shugaba Buhari karon farko a 2015, babbar matsalar tsaro da ake fuskanta ita ce ta Boko Haram wadda ke addabar Arewa maso Gabas.

Duk da cewa yanzu Boko Haram ba ta rike da wani yanki na kasar, karuwar garkuwa da mutane, da hare-hare masu alaka da siyasa, da rikicin manoma da makiyaya, da na ’yan bindiga, da kuma amfani da karfi fiye da kima daga jami’an tsaro na sanyaya gwiwar al’umma game da ikon gwamnati na tsaron lafiyarsu.

A yanzu matsalar ta yadu zuwa fadin kasar, ba Arewa maso Gabas kawai ba.

A tattaunawar Aminiya ta cikin shirin podcast na Najeriya A Yau da wani Detective Auwal Durumin Iya, ya ce babbar barazanar da ke iya kawo wa kasar nan zagon kasa ta fuskar zaman lafiya ita ce kabilanci da kuma bangaranci na addini.

A cewarsa, kabilanci da bangarancin addini su ne manyan matsalolin da ke rura wutar rikici ko’ina a fadin kasar Kudu da Arewa.

Haka kuma, Durumin Iya ya ce akwai manyan kalubale mabambanta da Tinubun zai fuskanta a Arewa da Kudu.

A bangaren Arewa, Detective ya ce akwai matsalar ’yan fashin daji da satar mutane domin neman kudin fansa, da rikicin makiyaya da manoma da kuma kwararar makamai da miyagun kwayoyi ta barauniyar hanya.

A Kudancin kasar kuma, ya ce akwai matsalar fasa bututu da satar danyen mai, da matsalar ’yan awaren Biyafara na IPOB da kuma masu kutse a Intanet da satar bayanai da kudi da ake kira ’yan yahoo.

Bangaren Ilimi

Daya daga cikin yara biyar wadanda ba sa zuwa makaranta a fadin duniya daga Najeriya suke, kamar yadda Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana.

Kasancewar kusan kashi 40% na yara ƴan shekara 5 zuwa 11 ba sa zuwa makaranta lamari ne mai tayar da hankali.

Wannan matsala ce da ta shafi kowane bangare na kasar, to amma ta fi kamari ne a arewacin kasar.

Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da suka ta’azzara lamarin, sai dai talauci da kuma bambancin jinsi na taka muhimmiyar rawa.

A tattaunawar dai ta cikin shirin na Najeriya A Yau da wani malamin makaranta da ya shafe shekaru yana koyarwa, Haruna Wada Adamu, ya ce dole akwai bukatar sabon Shugaban Kasa ya mayar da hankali wajen a bangaren saboda da tarin matsalolin da ya kunsa.

Malam Haruna ya ce ya wajaba a kan sabon zababben Shugaban Kasa ya tabbatar an inganta ilimin shi kansa sannan kuma saukaka hanyar nemansa, yadda da ’ya’yan talaka da mai kudi za su nema a lokaci guda.

Ya ce tilas ne sabon Shugaban ya rage adadin “out of school children” wato yawan yaran da ba sa zuwa makaranta musamman a Arewacin Najeriya.

Rikicin ASUU

Tsawon shekaru a Najeriya daliban jami’a da dama a kasar nan sun fuskanci koma baya a fagen karattutukansu sakamakon tijirar da ke tsakanin gwamnati da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

Galibi dai ASUU ta kan yi wa gwamnati bore ta hanyar shiga yajin aiki domin neman biyan bukatu daga bangaren gwamnati, wanda a wani sa’ilin hakan yake janyo rabuwar kai a tsakanin al’umma har a samu ana jifan kowane bangare da zargin halin ko in kula.

Ita ma dai wannan tankiyar a cewar Malam Haruna akwai bukatar sabon Shugaban Kasa ya kawo karshenta.

Malam Haruna ya ja hankalin Tinubu a kan kar ya kuskura ya yi zabin tumun dare wajen nada wadanda za su rike madafan iko a bangaren ilimi. “Dole a nada kwararru wadanda suka goge a fagen sanin ya kamata.”

An dai jiyo sabon Zababben Shugaban yana shan alwashin cewa daliban jami’a su sha kuriminsu domin kuwa yajin aikin ASUU ya zama tarihi tun da ya zama Shugaban Kasa.

Shugabannin Majalisar Tarayya 

A yayin da wasu zababbun ’yan Majalisar Tarayya ke ci gaba da fadi-tashin samun gindin zama domin cin gajiyar kujerar Shugaban Majalisar Dattawa da kuma ta Kakakin Majalisar Wakilai, Tinubu ya ce sam ba da shi ba a wannan fafutika.

A wani taron kusoshin jam’iyyar APC da ya gudana tare da duk zababbun ’yan Majalisar Tarayya na jam’iyyar a Dakin Taro na Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa, Tinubu ta bakin zababben Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce bai ayyana goyon bayansa ga kowanne daga cikinsu ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, masu neman shugabancin Majalisun Tarayyar na ci gaba da tuntubar takwarorinsu gabanin kaddamar da Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta 10 da za a yi a watan Yunin bana.

Daga cikin sanatocin jam’iyyar ta APC da ke hankoron kujerar Shugaban Majalisar Dattawan akwai; Barau Jibrin (Kano), da Godswill Akpabio (Akwa Ibom), da Orji Uzor Kalu (Abia), da Sani Musa (Neja) da kuma Dave Umahi (Ebonyi).

Haka kuma, a bangaren masu sha’awar kujerar Kakakin Majalisar Wakilan akwai; Ahmed Idris Wase (Filato); Muktar Aliyu Betara (Borno); da Aminu Sani Jaji (Zamfara).