✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalmar Godiya (1)

Kwanakin baya na hadu da wani dake ta gunaguni wai shi zafin rana ya yi yawa har ma ya fara wasu maganganun da bai kamata…

Kwanakin baya na hadu da wani dake ta gunaguni wai shi zafin rana ya yi yawa har ma ya fara wasu maganganun da bai kamata ba, bayan sa’o’i kadan kawai, sai ga ruwan sama kamar ana zubo wa da bakin kwarya. Ina jiran in ji ya ce Allah Ya ansa adu’arsa, sai ya fara cewa ai ruwan saman nan ya bata masa sha’ani, ruwan zai jika shi, ruwan zai hana shi tafiya gida, ruwan zai yi kaza, ruwan zai yi kaza. Yya dau lokaci mai tsawo yana ta surutai a maimakon ya nuna godiyarsa ga Ubangiji Allah. Haka nan a lokuta da dama mukan nuna rashin godiya ga Allah ta bangarorin rayuwarmu da dama.

A wannan mako za mu yi binchike ne akan godiya. Kamar yadda muka sani, mukan yi godiya duk lokutan da wani ya yi mana alheri ko wata kaykyawar kyauta. Mukan bude baki mu ce mun gode ko nagode. Lallai godiya kan kara karfin zumuta tsakanin mai yin alheri da mai karbanta. A nan zamu ga cewa dankon zumunci yakan kara karfi kwarai da gaske. Mukan gode wa iyayenmu da ‘ya’yanmu da abokanenmu har ma da shugabanin mu, amma muna gode wa Allah kwa? A gurguje zamu iya bada ansa, amma tambayar ita ce muna yin sa da zuciya daya ko kawai muna fada ne kawai da baki?
Bari mu duba me littafi mai tsarki ya fada kan godiya. A littafin Tasalonikawa ta fari, sura biyar aya ta goma sha takwas (1 Tasalonikawa 5:18) “Ku yi godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu”. Maganar Allah na cewa mu zama masu godiya ga Allah a cikin kowace halin da muka samu kanmu, dalili kuwa shi ne, Allah ne Ya hallice mu, Shi ya ba mu rai da iskar da muke shaka, Yana da sanin jiya, Ya san yau, Ya kuma san gobe da har abada, Shi ya hallici ranar da muke cewa na da zafi ko ruwan saman da muke cewa na bata mana sha’ani, to me ya sa ba za mu gode Masa ba? Ya yi rana ne domin mu mori rayuwa ta wurin haske, lafiyar jiki, amfanin gona da abubuwa da dama. Haka ma ruwan sama.
Bari mu ga wasu daga cikin dalilan da ya kamata mu zama masu godiya ga Allah:
1. Shaidar godiya daukaka ne ga Allah.
Cikin littafin Korantiyawa ta biyu, sura hudu aya goma sha biyar (2 Korantiyawa 4:15) “Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin Allah Ya yadu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, domin a daukaka Allah”. A nan mun ga cewa shaidar godiya na daukaka Allah, a duk lokacin da muka nuna godiyarmu ga Allah, wannan ma kadai tabbaci ne cewa akwai Allah, kuma muna nuna cewa mun dogara gare Shi. Godiya ta gaskiya na nuna cikkakiyar yarda cewa duk abubuwan da ke faruwa cikin rayuwar mu ko kusa da mu Allah na sane da shi kuma Yana da iko a kan sa.
2. Littafi mai tsarki ya bukace mu mu zama masu godiya.
Cikin littafin Zabura ta dari aya hudu (Zabura 100:4) Magana Allah na cewa; “Ku shiga HaikalinSa da godiya, ku shiga wurinsSa mai tsarki, ku yabe Shi! Ku gode maSa, ku yabe Shi!” sannan kamar yadda muka duba da farko cikin Tasalonikawa ta fari sura biyar aya goma sha takwas ( 1 Tasalonikawa 5:18) “Ku yi godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu”, na fari cikin Zabura, maganar Allah na kiran mu ne mu zama masu godiya da yabo ga Ubangiji, mu kuma daukaka sunan Sa, sannan manzo Bulus kuma cikin Tasalonikawa ta fari ya ce mu zama masu godiya a cikin kowane hali, don nufin Ubangiji ne zuwa garemu bayinSa ta wurin Almasihu Yesu.
3. Domin sakamakon rashin godiya na da muni.
Romawa sura daya aya ashirin da daya (Romawa 1:21) na cewa; “Domin kuwa kodayake sun san da Allah, duk da haka ba su daukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta”. Rashin godiya na sa mutum ya dogara ga kansa duk da yana ganin shaidar ikon Allah a ko’ina da kodayaushe, wannan kuwa yakan kawo gunaguni (kamar yadda muka ga wani ya yi akan zafin rana da ruwan sama) tare da bacin rai. Cikin littafin Ibraniyawa sura goma sha biyu aya goma sha biyar (Ibraniyawa 12:15) maganar Allah na cewa; “Ku kula fa, kada kowa ya kasa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen bacin rai ya tabbata, ya haddasa barna, har ya bata mutane masu yawa ta haka”, to da yake shaidar godiya na nuna aminciwar mu ne ga alheran Allah, gunaguni kuwa zai nuna rashin amincewar mu ne ga alherin Allah, zai kuma zama ba mu darjanta Allah ba a zaman Sa na Mahallicin dukkan duniya wanda kuma ke sane da dukan abin da ke faruwa da ita da cikin ta. Rashin darajanta Allah kuwa na tare da matsaloli da dama, domin haka sai mu lura, mu zama masu nuna godiya ga Allah a kodayaushe cikin kowane yanayi ta wurin yin haka kuma za mu nuna rayuwar mu cikin Almasihu Yesu.
Korantiyawa ta biyu, sura biyu aya goma sha hudu (2 Korantiyawa 2:14) “Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum yake yi mana jagaba mu ci nasara, albarkacin Almasihu, ta wurinmu kuma yake baza anshin nan, na sanin Almasihu a ko’ina”, to a zamanka na Kirista dole ne ka zama mai nuna godiya ga Allah a kodayaushe.
Tambaya, kana da ikon kara sakan daya a rayuwar ka?
Zan so in ci gaba da bayani daga wannan wuri mako mai zuwa idan Mai duka ya bar mu cikin masu rai. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.