Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana wasu kalamai da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi game da jam’iyyarsu ta PDP da cewa soki-burutsu ne.
Sule Lamido ya yi fatali ne da wani ikirari da Atiku ya yi a shafinsa na Twitter cewa “PDP abar misali ce wajen tabbatar da bin doka da tsarin mulki, lamarin da ya karfafi dimokuradiyyar Najeriya”.
“A ganina, PDP ba ta da hurumin da za ta iya yin wannan ikirari”, inji Sule Lamido.
- A karo na biyar, Atiku zai sake tsayawa takara a 2023
- Rikicin shugabanci: ’Yan sanda sun rufe hedikwatar APC
Tsohon gwamnan na Jigawa dai na cikin mutum 11 da Atiku Abubakar ya kayar a zaben fitar da wanda zai yi wa PDP takarar shugabancin kasa a 2018.
Atiku Abubakar ya wallafa kalaman da suka jawo wannan martini ne dai jim kadan bayan jam’iyyar APC mai mulki ta rushe Kwamitin Gudanarwarta ranar Alhamis.
Yi wa kai hisabi
“Ina fatan bin doka, da da’a, da biyayya ga kundin tsarin Mulki wadanda muka zama abin koyi da su a matsayinmu na jam’iyya za su yi jagora ga wasu jam’iyyun.
“Idan ba doka da oda a cikin gida, jam’iyya ba za ta iya samar da doka da oda a Najeriya ba”, inji Atiku.
Sai dai a cewar Sule Lamido,
“Rawar da muka taka a daidaikunmu kawai za mu yi nazari a kai mu gano cewa wannan [magana ta Atiku] soki-burutsu ce kawai.
“Idan muka yi wa kawunanmu hisabi, za mu ga kamanninmu na asali”, inji Sule Lamido.
Mutanen biyu dai na cikin kusoshin jam’iyyar PDP da ke da burin sake yin takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.