✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kai tsaye: Liverpool ta lallasa Manchester City da ci 2 da 1

Abin da za mu iya kawo muku ke nan a yau, sai kuma gobe, inda za mu kawo muku labarin wasa Realmadrid da Juventus kai…

Abin da za mu iya kawo muku ke nan a yau, sai kuma gobe, inda za mu kawo muku labarin wasa Realmadrid da Juventus kai tsaye. Da fata kun ji dadin labari.

Gabriel Jesus ne ya zura kwallo a minti biyu, wanda ya sa Man City suka fara tunanin za su lallasa Liverpool, amma kuma bayan an dawo hutun rabin lokaci, sai Salah da Firminho suka farke a minti 56 da 77. Wannan ne ya sa aka cire kungiyar ya Man City daga gasar cin kofn zakarun Turai na bana Abin kamar almara, amma kwallon kafa ta gaji haka.

A daya wasan kuma an lallasa Barcelo da ci 3 da nema. Yanzu dai an cire Man City da Barcelone ke nan.

Wasa ya kare.  Liverpool ta ci Man City gida da waje.. Cancanjaras.. Jimilla Liverpool 5 Man City 1

An kara minti biyu bayan minti 90 ya cika.

88: An canja Salah an sako Ings. Domin a kara masu kare gida..

87: Saura minti 3 kacal a tashi. Liverpool 2 Man City 1.

84: Har yanzu dai Man City 1 Lliverpool 2..

A daya wasan kuma, Roma na lallasa Barcelona da ci 3 d nema. Idan aka tashi haka, an cire Barcena ke nan.

80: Goallllllllllll… Man City ta zura kwallo na biyu. Amma Sane na cikin gidan Liverpool tsundun. Rafare na busa satar gida. Har yanzu dai Man City 1 Liverpool 2.

Jimilla Lliverpool 5 Man City 1. Man City. Gaskiya Man City na cikin matsala.

76: Goallllllllllllllllllllllllllllllllllllllllll… Firminhoooooooooooooooooooooooooooooooo… Ayyyyaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa…. Firminho ya zura kwallo na biyu.. Liverpool 2 Man City 1..

75:  Har yanzu dai Man City 1 Liverpool 1. Yanzu dai an fi taka kwallon ne a tsakiya.

58: Yanzu Man City na bukatar akalla kwallaye biyar ke nan. Hakan na nufin dole sai sun kara kwallo hudu, idan har Liverpool ba ta kara ba ke nan. Gaskiya da kamar wuya. Amma dai sai an tashi.

56: Goallllllllll… Salahhhhhhhhhhhhhhh.. Muhammad Salah ya farke. Sadio Mane ya janyo kwallon, cikin wuya da kyar da kyar har ya kawo cikin gidan Man City, daga karshe har ya fadi, inda shi kuma Salah ya tsinci dami a kala, sannan ya yi amfani da basira ya daga kwallon inda ta fada ragar Man City. Anya Man City za ta iya kuwa?

55: Yanzu Liverpool sun kwantar da hankalinsu suna taka leda

52: Kwallon yau ‘yar taka zura ce. Ba a taka leda yadda ya kamata. Man City ta taka leda (passing) 370 yayin da Liverpool ke da 171 kacal..

50:  Har yanzu dai Man City 1 Liverpool 0

An dawo bakin daga..

An tafi hutun rabin lokaci: Manchester City 1 Liverpool 0. Sai an dawo hutu za mu ga yadda za ta kaya.

41: goalllll.. Man City da zura kwallo na biyu.. kash! rafare ya busa satan gida.. har Sane ya fara murna. amma rafare ha hana.
40: Goalllllllllll… kash! kwallon ya buga sandan fos.. saura kiris Bernado Silva ta ci.
38: Bernado Silva ya kai hai hari mai kyau, amma ina, kwallon ta bude da yawa.
34: An ba Firminho katin gargadi saboda ya kwada De Bruyne da kasa. Yau dai da alamu za a samu kati da yawa. Allah kiyaye kada a samu jan kati.
Tarihi: Ba a ci Liverpool ba a wasa biyar da suka wuce da suka buga a waje. Ko yau za a farke musu laya?
17: Har yanzu Liverpool ba tai hari ba. Amma dai wasan na zafi sosai.
14:  An ba Sadio Mane da golin Man City Ederson katin gargadi.
9: Liverpool ta kai hari mai kyau, amma ba sa’a.
2: Goallllllllll… Man city ta zura kwallo a ragar Liverpool. Man City 1 Liverpool 0. Gabriel Jesus ne ya zura kwallon. Lallai fa yau akwai kallo.
Yanzu haka an fara taka leda, kuma Man City sun fara da karfinsu.
‘Yan benchi: Clyne, Klavan, Moreno, Mignolet, Ings, Solanke, Woodburn.
Liverpool (4-3-3): Karius; Alexander-Arnold, Lovren, Van Dijk, Robertson; Oxlade-Chamberlain, Milner, Wijnaldum; Salah, Firmino, Mane.

‘yan banchi: Bravo, Kompany, Gundogan, Aguero, Delph, Zinchenko, Foden.

‘Yan wasa:

Manchester City (3-2-4-1): Ederson; Walker, Otamendi, Laporte; Fernandinho, De Bruyne; Sterling, Bernardo Silva, David Silva, Sane; Gabriel Jesus.

 

 

Yau za kece raini tsakanin kungiyar Manchester City da Liverpool a zagaye na biyu na wasan zakarun Turai.

A zagaye na farko na wasan, Liverpool ta doke Manchester City da ci 3 da nema. Yau ke nan Manchester na bukatar akalla kwallaye 4, idan har Liverpool ta gaza zura kwallo ke nan.

Mai sharhi a kan wasanni, Ahmad Garba Muhammad ya ce yana tunanin Guordiola da Manchester za su bata lokacinsu ne kawai, domin sun riga sun bar shiri tun rani.

Ku biyo anjima domin samun labarin wasan kai tsaye a lokacin da ake bugawa.  Za a fara wasan ne da misalign karfe 7 da minti 45.