Salallamin sauke Salami
Sallamar mai mukami
Babu daukar makami
Watsattsake ne da alkalami
A dai kwace damin burgami
Kotun kwaram-kwandon
Tuhumar boye matsabbai a lungu
Sai ta dauro mutum a kugu
Kwaramniyar shan dundun
Dudun-dundun
Salalar salular sili-tili
Santalar Santali
Subul da bakan tonon silili
Shaci-fadin rashin hankali
Shashancin shari’ar shagali
Masu dibar dukiya sui fatali
Su daure mai kin biyan jangali
Komarsu na walwali
Nau’ukan kifaye akai wa fasali
Batun ga ba aiki da hankali
An yi Audu Awon-doka
An yi Adoke Doka
Makalutun Malami
Sai ka kara kaimi
Don ka da kowa ya koka
Kagen kunduge kwangen kwage
Dungun dudduge
Durgu ya dage
Dukiya an kange
Kariyar kwandon Barau aka buge
Bera na tsoron mage
Sauro ya sagale a sange
Batun ingarma babu kage
Mai kiren karya ya doge
Cincin karfi ya daddage
Laulayin doka
Tabargaza an tafka
Takun turka-turka
An yi kiki-kaka
Mai shari’a na bin Dan-wanka
Bambamin baka
Bankade-bankaden bukka
An dai samu baraka
Rashin bin ka’ida ya cuceka
Ka dai kammala naka
Bugewar barcin mai dokar gyangyadawar kotun kwance wa kasa takaddamar shari’o’i ta sanya ni cikin SALLAMIN SUKAR SAUKE SALAMI da aka taba tsuwurwurtawa a shigafar daukaka kara ta tarayyar Haorobiya. Kai hasali ma har wassafawa na yi a tunanina kan yadda Gwamnatin Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki ta wancakalar da Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi daga jan ragamar Babban Asusun Asin Kasa. Shin wadannan al’amura an aiwatar da su ne bisa tanade-tanaden dokoki ko kuwa dukan ta-mola aka yi wa dokokin kasa, don a cimma soye-soyen zukatan masu mulkin mulaka’un Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge?
Ba tare da na samu amsar tambayar da na bijiro da ita ba, ina ganin hayagagar yunkurin tsige mai shari’ar da ya yi SHIRMEN SHARRI, wajen yin kwange da kundume matsabbai wai shi ga kwage, ai ba ta kamata a bari ya sha ba. Domin in aka ci gaba da tsuwurwurta irin wannan kwakyariyar KWASHI-KWARAF ana lakume tuwo, an sha miya SHARKAF, ai sai miyagu su ji dadin tafka ta’asa.
Haurobiyawa kada a yi mana DAMFARAR DAMUN FURA, har ta sanya kawunanmu FURFURA ba tare da mun fasko inda aka dosa ba. Ya kamata dai kowa ya hau kurku-rido mai zuwa Gano, ko ma in ta kama a yanki tikikin tsuntsun sama don yin balaguro zuwa kasar Ghana wajen yin gane-gane. Ta’asar da babban kwabo ya tafka a kwanon tasarsa, lakabinta shi ne, “KAGEN KUNDUGE KWANGE KWAGE.
Bisa la’akari da irin tufka da warwarar da ake ta tafkawa, kan lamarin mai shari’ar kolin koliyo a Haurobiya, ina ganin gara a yi mai yiwuwa tun kafin lokacin ya kure. Domin kasashen duniya da dama sun tsige irin wadannan bara-gurbin da ke cutar da al’umma, koda kuwa kuskure suka yi, ballatana ma da kansa ya yi ikrarin kakaba wa kurungunsa TAGIYAR MALAM MANTAU, wai sai yanzu da aka bijiro da tabargazar da ya tafka, sai ya yi wuf ya ce, an kakaba masa TAGIYAR MALAM TUNAU.
Lallai mu ja na-zomon kafafen yada kwakwazo da akwakun wulkitawar hotuna da baje batutuwan kasa, su daina iza wuta. Abin da kawai ya kamata mai mukamin duk da ya san cewa ya yi aika-aika, musamman yi wa DOKA KARAN-TSAYE, to wajibi ne ya sauka daga mukami ba tare da an yi wani ka-ce-na-ce ba. Kuma duk inda aka samu managartan hujjojin da suka wanke wanda duk ake tuhuma da aikata laifuffuka, a iya SOLLE SHI/TA SOL DA SABULUN SALO a dawo da shi/ta kan mukaminsa/mukaminta. Idan kuwa aka samu akasin haka, wato mai laifi ya yi DUMU-DUMUN DAMA-DAMAR DAMAWA, sai kawai a damke shi/ta, a yi masa/mata kamun kazar kuku ko daurin goro goriya a huhu.
’Yan makaranta ina fatan mun fasko UNGON-GOGE mai BURGAMIN-BUGE, wanda ya yi wa doka karan-tsaye, lokacin da ya yi wa Malam Mantau fintinkau, bayan da Malam Tunau ya sha gabansa, sai ya zo daga bisani yana cewa, “ashe-ashe AU-AU!”
Haurobiyawa mu yi karatun ta-nastu, tare da kauce wa al’amuran da ka iya haifar wa kasa mutsu-mutsu, har ta kai ga gama-garin mutane su yi ta tsuwwa tsu-tsu tamkar za su tashi sama kamar tsuntsu.