✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafin a janye tallafin man fetur

A  kwanakin baya mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya a kan lallai ta gaggauta janye tallafin man…

A  kwanakin baya mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya a kan lallai ta gaggauta janye tallafin man fetur, kuma ta kara karya darajar Naira. Duk da wadannan kiraye-kiraye, ba sababbi ba ne a kasar nan, amma dai kungiyar kwadago ta kasa, wato NLC da ta masu yin kayayyakin masana`antu, wato MAN da daidaikun mutane, na cikin wadanda suka yi dirar mikiya a kan Mai martaba San Kano, a kan wancan lokaci, har suna fassara kiraye-kirayensa da rashin tausaya wa talakawan kasar nan a kan irin bakin kuncin rayuwar da suke ciki ta rashin abin hannu, ga shi kuma kiraye-kirayen nasa za su kara jefa talakawan cikin wani kuncin rayuwar.
Bayan wancan kira na Mai martaba Sarkin Kano, kwatsam kuma a ranar Talatar da ta gabata sai ga Bankin Duniya a wani rahotonsa na tattalin arziki da ya fitar, ya fito karara yana shawartar Gwamnatin Tarayya da lallai ta janye tallafin man fetur din, a yanzu kasancewar farashin danyen man fetur ya yi faduwar da bai taba yi ba, har Bankin Duniya ya kara da cewa, babu wasu alamu da suke nuni da cewa, farashin  man fetur din zai iya farfadowa. Ra’ayin rahoton Bankin Duniya ne cewa, muddin kasar nan ta ci gaba da daukar dawainiyar biyan tallafin, to kuwa nan da shekara uku masu zuwa wato 2018, kasar za ta kashe kashi 30 cikin 100, na yawan kudin shigarta a kansa.
Mista John Panzer, Babban Darakta mai kula da fannin tattalin arziki na kasa-kasa da tafiyar da kashe kudade na Bankin Duniya da ya gabatar da rahoton a Abuja, ya kara da cewa, idan har kasar nan za ta iya janye tallafin man fetur din a yanzu, farashin man ba zai wuce Naira 100 a  kowace lita ba. Abin da ya ce, yanzu duk da tallafin, rahotanni daga Hukumar kididdiga ta kasa, daga sassan kasar nan daban-daban suna tabbatar da cewa, jama’a na sayen man fiye da Naira 100, a kan kowace lita. Rahoton Bankin Duniyar, ya ce a ’yan shekarun nan, rahotannin binciken yadda gwamnati ke kashe kudinta, ya gano cewa, biyan kudin tallafin cike yake da cin hanci da rashawa da sama da fadi iri-iri. Rahoton Bankin ya ce tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014, kasar nan ta kashe Naira tiriliyan bakwai, wajen biyan kudin tallafin man fetur din.
A kasafin kudin bana Naira biliyan 143, Majalisar Dokokin kasar nan ta amince da su kudin da za a biya a zaman tallafin, amma a yanzu maganar da ake a kwanan nan Majalisar Dattawa ta amince wa Gwamnatin Tarayya ta sake biyan wasu kudin a zaman tallafi da suka kai Naira biliyan 522. Yayin da a kasafin kudin shekara mai zuwa na sama da Naira tiriliyan shida da koyaushe ana iya mika shi ga Majalisar Dokokin kasa akwai tanadin Naira biliyan 150, don biyan kudin tallafin man na wannan shekarar da muke ban kwana da ita. Mai karatu na bar ka ka lissafa irin yawan kudin da tallafin yake lakumewa da suka zame wa Gwamnatin Tarayya alakakai, ta yadda kullum tana cikin biyan bashinsu.  
A makon jiya haka shi ma Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Muhammadu Ali Ndume, ya bi sahun masu zargin cewa kudin tallafin da ake biya, ba na hakika ba ne, inda aka ruwaito shi yana cewa, fiye da rabin Naira biliyan 522 da suka amince a biya kwanan nan a zaman tallafin ba na gaskiya ba ne, yana mai cewa, sau tari masu shigo da man sukan yi amfani da biyan tallafin don su bata sunan ’yan kasar nan, ko su jefa su cikin wahala. Sanata Ndume, ya ce “A duk lokacin da wadanda suke shigo da man suka bushi iska, sai su daina samar da shi, kafin ka ce kwabo, sai ka ga dogayen layukan ababen hawa sun dawo, nan da nan sai abubuwa su fara ta’azzara a cikin kasa. Da wannan ala tilas sai gwamnati ta fara biyan kudin tallafin na gaskiya da na karya,” in ji Sanata Ndume.
Sama-da-fadin da ake cikin biyan kudin tallafin man fetur din, kamar yadda na ce ba wani sabon labari ba ne, a kasar nan kamar yadda ta bayyana daga kwamitin tsohon dan Majalisar Wakilai, Alhaji Faruk Lawan da majalisar ta kafa a shekarar 2013, don ya bi mata diddigin yadda ake biyan kudin tallafin da irin almundahanar da ake yi a ciki, bayan Gwamnatin Tarayya ta yi karin farashin man daga Naira 65, a kan kowace lita zuwa Naira 140, a karshen shekarar 2012 da sunan ta janye tallafin, amma kazamar zanga-zangar da aka yi cikin kasa ta tilasta wa gwamnatin ta mayar da shi Naira 97, a kan kowace lita. Kowa dai ya san daga karshe aka samu Faruk Lawan da sakatarensa da hannu dumu-dumu, wajen karbar hancin Dala dubu 620 daga hannun shaharren mai hada-hadar man fetur din nan, Mista Femi Otudola da sunan kwamitin zai tsame sunan kamfaninsa daga cikin wadanda ya gano suna sama-da-fadi kan kudin tallafin. Batun zargin karbar cin hancin da yanzu ya ke gaban kotu.
Da irin wannan wahala da fargaba uwa-uba tabarbarewar tattalin arziki da wannan tallafi  kullum yake kara jefa mafi yawan ’yan kasa, ni ma ina da ra’ayin yanzu ne Gwamnatin Tarayya ya kamata ta janye hannunta a kan wannan tallafi da a kullum take cewa tana yi wa talakawan kasar nan, alhali wasu ’yan tsiraru suke amfana. Batun janye tallafin man fetur da na takin zamani su ne batutuwa biyu da a wannan fili na dade ina begen ganin an yi, ko talakawan kasar nan za su samu sa’ida, a kuma daina yi musu gorin ana tallafa musu. Amma kafin a janye tallafin man fetur ya kamata Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wajen gyara dukkan matatun man fetur hudu da muke da su a kasar nan, sannan ta karfafa wa ’yan kasuwar ciki da wajen kasar nan gwiwa a kan yadda za su zo su zuba jari, don kakkafa matatun man fetur, ta yadda tace man a cikin gida zai rika zama a wadace, kuma da arha. Don kuwa batun ba na ba mu da danyen man ba ne.
Haka zalika ta kara mayar da hankali wajen sarrafa iskar gas din da muke da ita, wadda samuwarta a wadace zai iya inganta samar da wutar lantarki da muke matukar bukata don farfado da manya da matsakaita da kananan masana’antunmu da za su samar da dimbin ayyukan da ake bukata. Haka batun farfado da duk fannonin ayyukan noma da kiwo da yanzu Gwamnatin Tarayya ta fara da shirin farfado da noman alkama da shinkafa. Wannan fanni bai kamata gwamnatin ta ci gaba da yin sakaci da shi ba, musamman da yanzu ta tabbata cewa, koda man fetur bai kare ba, farshinsa zai yi ta faduwa kasa warwas.