An samu muhimman fa’idoji biyu daga ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari ta mako guda a kasar Sin, inda a karshen makon da ya wuce al’amarin da ya fi daukar hankalin al’umma, shi ne, rattaba hannu ranar Talatar da ta wuce kan yarjejeniyar hada-hadar ciniki da kudin Yuan. An rattaba hannu ne a birnin Beijing tsakanin Bankin Ciniki da Masana’antu na China (ICBC), wanda shi ne babban banki a kasar Sin, kuma wanda ya fi kowane bayar da rance a duniya, da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN), inda Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban kasar Sin di Jinping suka zama shaidu wajen bikin rattaba hannun.
Watya babbar fa’idar ziyarar ta buhari kasar Sin, ita ce ta samun bashin Dala biliyan shida don cike gibin kasafin kudi, wato Naira tiriliyan biyu da biliyan 200 (Dala biliyan 11 da miliyan 100). Lin Songtian Darakta-Janar mai kula da harkokin Afirka a Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin, ya ce, dangane da hada-hadar kudin musaya, “wannan na nufin kudin renminbi (Yuan) zai bazu a bankunan Najeriya daban-daban, sannan za a cusa renminbi a rukunin kudin musaya na ajiyar Najeriya ta kasashen waje.”
Shirin musayar kudi da kasar Sin na da matukar alfanu wajen fuskantar kalubalen da ke tunkarar kasar nan a daidai lokacin da aka samu faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, da dimbin kudin musayar waje na Najeriya suka yi matukar raguwa. Ministar kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta ce gwamnati na duba yiwuwar saka jari a kullin dukiyar bashin Panda (Panda bonds). Wadannan nau’ukan kullin dukiya ana yin hada-hadar su ne cikin kudin renminbi, kuma a yi hada-hadar kasuwancin su a cibiyoyin hada-hadar kasashen waje na Sin. Duk da cewa ba a bayar da cikakken bayani ba, wannan tsari na da matukar arha wajen gudanarwa, in an kwatanta da kullin dukiyar bashinTurai ta “Euro-bonds,” sai dai akwai dar-dar da yin kaffa-kaffa da masu saka hannun jari daga Turai wajen nuna kiyayyar su ga tsarin hada-hadar kudade ta Najeriya, al’amarin da suke ganin zai kawo tarnaki ga samun nasarar hada-hadar kullin dukiyar bashin Turai “Euro-bonds.” Gwamnati dai ta yi abin da ya dace wajen samun mafita.
Duk da cewa babu cikakkun bayanai, abin da kawai aka fahimta shi ne kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar Sin zai sauka daga kan musayar Dala da ta zama dole. Wannan zai sanya a rage neman Dala daga Babban Banki, kuma kasancewar kasar Sin babbar kasar da ake shigo a kayyaki zuwa Najeriya. Sai dai akwai wasu al’amura da shirin ya bijiro da su. Na farko dakile amfani da Dala zai bunkasa kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar Sin, sannan ya bunkasa yawan kayayyakin da za mu shigo da su daga kasar Sin. Irin wannan alfanu zai sanya gwamnati ta kara kaimi wajen inganta masana’antun cikin gida.
A shekarar 2015, an kiyasta rarar ajiyar mu da gibin Dala biliyan takwas da miliyan 800. A kuma iya cewa, ba ma fitar da kayayyaki waje, da za su iya biyan kimar abin da muke shigowa da shi. A shekarar 2014, manyan kasasen hadin gwiwarmu wajen shigo da kayayyaki, su ne Sin mai kaso 25.3 cikin 100; da Amurka mai kaso 9.7 cikin 100 da Indiya mai kaso 4.7 cikin 100. Abubuwan da muka fi shigowa da su, su ne na’urori da sinadarai da motocin sufuri da kayayyakin da aka kera a masana’antu da abinci da dabbobi masu rai. Muna fatan gwamnati za ta mayar da hankali kan harkokin noma da hakar ma’adanai, al’amarin da zai iya taimakawa wajen cire abinci da sinadarai daga jerin kayayyaki (da ake shigowa da su). Ministar Kudi ta ce za mu fara fitar da tumatirin da aka sarrafa a bana, sannan shinkafa kuwa nan da shekarar 2018.
Shirin musaaayar kudin bai yi mana sako-sako ba, wajen yin aikin tukuru don neman kudin Yuan da za mu biya kudin kayyakin da aka shigo mana da su daga Sin. Wannan na nufin dole mu kara yawan kayan da muke kaiwa kasar Sin. Sannan akwai bukatar yin aiki tukuru da managarcin tsarin da zai zakulo nau’ukan kayayyakin da ke da kimar daraja a kasar Sin da sauran kasuwanni. Wannan bashin Dala biliyan shida na kasar Sin, ala’amari ne da zai yi ta kai kawon tunani a kawunan al’umma. Shin me kasar Sin ke son cimmawa? kasar Sin dai ba ta da lalitar kyautar kudi, domin ba za ta biya kudin aiwatar da ayyukan raya kasa a Najeriya don kawai ta daga tattalin arzikin Najeriya, ba tare da kasar ta dogara da ita ba, wajen shigo da kaayyaki ba, har sai ta kintaci dimbin alfanun da za ta iya samu a wasu fannonin.
Duk da cewa kasar Sin ba ta da wata mummunar manufa, ta bayyana karara sun yi shirin kafa kan su, yadda za a rika damawa da su a hada-hadar tattalin arziki mafi girma a Afirka, don samun alfanu nan gaba. Za a iya tantancewa ne idan an yi la’akari da yadda kasar Japan ta zuba dimbin jari a masana’antun kasashen Kudu maso Gabashin Asiya. A halin yanzu ita ke jan ragamar kasuwar na’urorin ababen hawa. Ta samu karin kudin kwadago a gida, shi yasa yake da fa’ida ga kasar Sin ta samu wasu wurare daban na aiwatar da ayyukanta. A daidai lokacin da muke murnar fa’idojin da muka samu, muna ganin akwai bukatar gwamnati ta yi amfani da kwararru wajen yin hasashen makomarmu. Mun sha kulla yarjejeniya da kasashen Turai na tsawon shekaru, don haka bai kamata mu sauya ubangidan da bayi ke yi wa bauta ba, da wani ubangida, ko ma wasu masu dimbin yawa.
Kafin a fara hada-hadar Yuan
An samu muhimman fa’idoji biyu daga ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari ta mako guda a kasar Sin, inda a karshen makon da ya wuce al’amarin da…