Biyo bayan matsayar da Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta cimma, gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin bincike domin duba zargin cin zarafin al’umma daga jami’an ‘yan sanda a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun Mai Ba Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Watsa Labarai, Muyiwa Adekeye a ranar Juma’a.
- #EndSARS: Za a kori ‘yan sanda 37, a gurfanar da 24
- Kotu ta soke daukar ‘yan sanda 10,000 da aka yi a 2019
Sanarwar ta ce a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba za a rantsar da kwamitin mai mutane bakwai wanda zai kasance karkashin jagorancin tsohon mai shari’a David Shiri Wyom, sai AIG Lawal Tanko mai ritaya a matsayin mamba yayin da Rebecca Sako-John da kuma Mustapha Jumare za su wakilci kungiyoyi masu zaman kansu.
Idan dai za a iya tunawa NEC ta umarci dukkan gwamnonin jihohi da su kafa kwamitocin a matsayin matakin farko na tsaftace aikin ‘yan sanda a jihohinsu.
Muyiwa ya kuma ce Yakubu Umar Ibrahim zai wakilci kungiyoyin dalibai a kwamitin, sai Nathaniel Sheyi Bagudu da Inna Bintu Audu da za su wakilci kungiyoyin matasa da na Hukumar Kare Hakkin Bil’Adama.
Sanarwar ta kara da cewa mai rikon mukamin darakta a sashen kalu da hakkokin ‘yan kasa na Ma’aikatar Shari’a ta jihar, Hajara Abubakar za ta wakilci Babban Lauyan Gwamnatin jihar a kwamitin.
Muyiwa ya kuma ce, “Za a kuma nada wakilan kwamitin kungiyoyi masu zaman kansu da na matasa domin su yi aiki kafada da kafada da gwaman jihar da sauran shugabannin tsaron jihar da zai sa ido kan ayyukansu.
“Hakan kuma zai biyo bayan nadin mambobin kwamitin kare hakkin Bil’Adama da kuma tura wadannan jami’an zuwa ofisoshin karbar korafe-korafe domin a ba jama’a damar su mika koke-kokensu kan jami’an ‘yan sandan domin a magance, su’’ inji shi.