Sabbin shugabannin Ƙananan hukumomin da Kansiloli da aka zaɓa a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kaduna da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, sun karɓi shaidar lashe zaɓe.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta mika takardun shaidar ga zaɓaɓɓun shugabannin .
Idan dai ba a manta ba zaɓen ƙananan hukumomi ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar, yayin da jam’iyyun adawa suka yi watsi da sakamakon da hukumar zaɓen jihar ta bayyana, wanda ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ce ta lashe dukkan kujerun ƙananan hukumomi da kansiloli.
A yayin gabatar da takardun shaidar a hedikwatar hukumar da ke Kaduna, shugabar KAD-SIECOM, Hajiya Hajara Mohammed, ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen a faɗin jihar kamar yadda dokar zaɓe ta jihar Kaduna ta 2024 ta tanadar.
Ta jaddada cewa, wannan shi ne karo na shida da hukumar ke gudanar da zaɓuka tun bayan kafuwarta a shekara ta 2000, amma musamman ma, wannan shi ne karon farko da zaɓaɓɓun shugabannin za su miƙa mulki ga zaɓaɓɓun shugabannin, lamarin da ya sa taron na yau ya zama tarihi.
Ta ce, “Na yi matukar farin cikin kasancewa cikin wannan gagarumin biki; rana ce ta tarihi, inda ake bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga waɗanda suka yi nasara a zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 da aka kammala.