✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada soyayyarmu ga Annabi ta tsaya a fatar baki (2)

Daga hudubar Muhammad Habibullah Muhammad Shakidiy Fassarar Salihu Makera   To sai dai ya ku bayin Allah! Mene ne matsayinmu a yau? Wajibi ne mu…

Daga hudubar Muhammad Habibullah Muhammad Shakidiy

Fassarar Salihu Makera

 

To sai dai ya ku bayin Allah! Mene ne matsayinmu a yau? Wajibi ne mu tambayi kawunanmu: Shin muna son Manzon Allah (SAW) so na gaskiya, ko kuwa muna fada ne kawai a baki?  Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dayanku ba ya zama mai imani, har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga mahaifinsa da dansa da dukan mutane.” Kuma Umar bin Khaddabi (RA) ya taba cewa: “Ya Manzon Allah! Wallahi kai ne mafi soyuwa a gare ni baya ga raina. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ba haka ya kamata ba. Na rantse da Wanda raina Yake hannunSa, (ba za ka zamo mai imani ba) sai na kasance mafi soyuwa a wurinka daga ranka.” Sai Umar ya ce: “Lallai kai a yanzu wallahi kai ne mafi soyuwa a wurina daga raina!” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Yanzu ne (ka yi imani) ya Umar!”

Mu tuna Abubakar Siddik (RA) wanda ya rika kukan farin ciki lokacin da ya ji cewa shi ne abokin tafiyar Manzon Allah (SAW) a yayin hijirarsa. A kan hanyarsu ta hijira idan ya tuna za a kawo hari ta gaba, sai ya koma gabansa (SAW), idan kuma ya tuna za a biyo su ta baya, sai ya koma ta bayan Manzon Allah (SAW), har suka isa Madina yana mai fansar Annabi (SAW) da ransa!

Sannan mu tuna Nusaiba ko Nasibatu bintu Ka’ab Al-Maziniyya Ummu Ammara (RA), mace ce da ta dauki takobi tana kare Manzon Allah (SAW) a lokacin da maza suka guje daga gare shi. Ya taba ce mata: “Tambaye ni abin da kike so Ya Ummu Ammara.” Sai ta ce: “Ina rokonka in kasance makwasbciyarka a Aljanna da sonka a duniya da sonka a Lahira!”

Sannan da aka kammala Yakin Uhudu sojojin Annabi (SAW) sun wuce ta wurin wata mace a hanyarsu ta dawowa Madina alhali an kashe mijinta da dan uwanta da mahaifinta, amma da aka yi mata ta’aziyya sai ta ce: “Me ya samu Annabi (SAW)? Suka ce ba komai sai alheri ya ummi wane! Yana nan lafiya bisa godiyar Allah kamar yadda kike so.” Sai ta ce: “Ku nuna min shi in gan shi. Sai aka yi mata ishara zuwa gare shi, a lokacin da ta gan shi sai ta ce: “Duk wata masifa a bayanka (in ba ta shafe ka ba), karama ce!”

Kuma lokacin da Kuraishawa suka aika Urwatu bin Mas’ud As-Sakafiy (RA) lokacin yana mushiriki a yayin Sulhun Hudaibiyya, da ya ga irin son da sahabbai suke masa (SAW) da ya koma zuwa ga Kuraishawan ce musu ya yi: “Ya ku mutanena! Wallahi hakika na bakunci sarakuna, na bakunci Kaisar da Kisra da Najjashi, wallahi ban ga wani sarki ko shugaba daya da mutanensa suke girmama shi kamar yadda sahabban Muhammad suke yi ga Muhammadu ba. Wallahi bai tofar da kakinsa face ya fada a tafin hannun wani namiji daga cikinsu ya shafe shi a fuskarsa da jikinsa. Idan ya umarce su sai su yi gaggawar aiki da umarnin. Idan yana alwala kamar za su yi fada kan neman ruwan alwalarsa. Idan yana magana sukan yi shiru, kuma ba su iya daga ido su kalle shi saboda girmamawa gare shi!”

Wannan shi ne son sahabbai ga Manzon Allah (SAW). Shin mu muna son Manzon Allah (SAW) ko dai al’amarin ya tsaya ne a da’awar baka kawai? Shin muna girmama shi? Shin muna yada Sunnarsa? Shin muna ladabtuwa da ladubbansa? Shin muna koyi da shiriyarsa?

“Lallai Mu, Mun aike ka, kana mai shaida, kuma mai bayar da bushara kuma mai gargadi. Domin ku yi imani da Allah da ManzonSa, kuma ku girmama shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) safiya da maraice.” (K:48:8-9).

Allah Ya yi min albarka da ku cikin bin Alkur’ani Mai girma. Kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da Ambato mai hikima. Ina fadin wannan magana tawa, ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai ne Shi, Shi ne Mai gafara Mai jin kai.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan mafi girman Annabawa da Manzanni.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Son Annabi (SAW) akida ce da dukkan Musulmi suka hadu a kanta duk da bambance-bambance kungiyoyinsu da fahimtarsu. Kowace kungiya ko fahimta tana zuwa ta hadu a kan sonsa (SAW), domin haka ya wajaba a kanmu mu farfado da wannan dabi’a a wannan duniya da take dada cin zarafi da batunci ga martabarsa (SAW) ta wajen hada kan al’umma da yin magana da murya daya wajen kare Manzon Allah (SAW). Wajibi ne mu yada girmama Manzon Allah (SAW) da sanar da ’yan baya kan kyawawan dabi’unsa. Wajibi ne a kan iyaye mata su raini ’ya’yansu kan son Manzon Allah (SAW). Wajibi ne iyaye maza su sanya ilimantar da ’ya’yansu tarihi da sirarsa a cikin manyan darussan da za su mayar da hankali a kai. Wajibi ne a kan malaman zaure da na makarantun zamani su kebe wasu lokuta don koyar da tarihinsa mai tsarki (SAW). Shin muna da wani lokacin da za mu hadu ne a irin wannan lokaci na yawan rarrabuwa fiye da fursar da zukata za su hadu a yi kokarin kare Manzon Allah (SAW)?

Yanzu ne lokacin da zai zama na sa’ada a ga mun zage dantse a daidaiku da kungiyoyinmu da hukumominmu muna yin abu daya wato kare Manzon Allah da tsare mutuncinsa (SAW). Ya wajaba a kanmu mu rika nuna sonmu ga Manzon Allah (SAW) da nuna fushinmu kan taba mutuncinsa, mu yanke hulda ko dangantaka da wadanda suke cin zarafinsa (SAW), mu daina yi duk wata mu’amala da su, mu daina sayo komai daga gare su.

Ya Hayyu! Ya Kayyumu! Ya Wahidu! Ya Ahdu! Ya Fardu! Ya Samadun! Ya jabbarus samawati wal ardi! Ya Sari’ul intikami! Ya Ubangiji! Ka nuna mana wa duk wanda ya baci Annabinka abubuwan mamaki na ikonKa. Ya Ubangiji! Ka shanye hannunwansu, Ka karyar harsunansu, Ka makantar da basirarsu da gannansu. Ya Ubangiji! Ka sanya su zama abin nuni a duniya. Ya Ubangiji! Ya Wanda Yake da izza da daukaka! Ya Wanda Yake da iko da kamala! Ya Wanda Shi ne Mai girma Madaukaki! Ya Ubangiji! Kada Ka bar tutarsu a tsaye, Ka sanya su da wadanda suke bayansu su zamo aya. Ya Ubangiji! Mun hada Ka da su, kuma Kai Mai iko ne a kansu!