Shugaban kasar Turkiyya Malam Recep Tayyip Erdogan ya ce tsarin iyali da amfani da kwayoyi ko allurar takaita haihuwa ba su dace da iyalin Musulmi ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ne ya ruwaito Shugaba Erdogan yana bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, furucin da ke goyon bayan kara hayayyafa kuma ya fusata masu rajin kare mata.
Shugaba Erdogan ya ce aikin iyaye mata ne su tabbatar da karuwar yawan iyali a kasar Turkiyya wadda jama’arta suka karu da kashi 1.3 a shekarun baya-bayan nan.
“Ina fadi balo-balo…akwai bukatar mu kara yawan hayayyafa. Mutane suna magana kan rage haihuwa da tsarin iyali. Babu iyalin Musulmi da zai fahimci haka kuma ya karbe shi,” ya fadi haka ne a Istanbul.
Ya kara da cewa: “Kamar yadda Allah da kuma Annabi mai girma ya ce, haka za mu yi. Kuma a wannan bangare shi ne aiki na farko da ke kan iyaye mata.”
Erdogan da matarsa Emine sua da ’yaya hudu maza biyu mata biyu, kuma a farkon wannan wata ya halarci wani babban bikin aure na kanwarsa Sumeyye da wani mai harkokin masana’antu tsaro Malam Selcuk Bayraktar.
Sannan kanwarsa Esra, wadda take auren mutumin da zai zama Ministan Makamashi, Berat Albayrak, tana da ’ya’ya uku.
Sai dai wata kungiyar kare hakkin mata mai suna The Platform to Stop biolence Against Women, ta soki kalaman na d Erdogan inda ta ce suna tauye hakkin mata.
“Kai (Erdogan) ba za ka iya tauye ’yancin mata na takaita haihuwa ba, ko ’yancinmu ta hanyar kalamanka na irin mutanen da,” kungiyar ta fadi ta shafin Tweeter dinta.
A shekarar 2014, Erdogan ya bayyana kayyade iyali da “cin amana” da ka iya jawo daukacin al’umma “ta kare.”
Ya rika kira ga iyaye mata su rika haihuwar akalla ’ya’ya hurhudu yana mai cewa: “da daya na nufin kadaici, biyu na nufin kishiyoyi, uku na nufin daidaito, yayin da hudu ke nufin yalwa.”
Ofishin kididdiga na kasar ya nuna cewa yawan al’ummar Turkiyya ya karu zuwa miliyan 78 da dubu 741 a bara, yayin da a shekarar 2000 kasar ke da mutum miliyan 68.
Kada Musulmi su amince da tsarin iyali – Shugaban Turkiyya
Shugaban kasar Turkiyya Malam Recep Tayyip Erdogan ya ce tsarin iyali da amfani da kwayoyi ko allurar takaita haihuwa ba su dace da iyalin Musulmi…