✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada mu yarda da masu ta da fitin su tsere – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce masu kiraye-kirayen wargaza Najeriya suna neman kai mu bango bayan da suka wuce gona da iri, inda ya ce…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce masu kiraye-kirayen wargaza Najeriya suna neman kai mu bango bayan da suka wuce gona da iri, inda ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe kan batun kasancewar kasar nan a dunkule.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa ga jama’ar kasa a ranar Litinin da ta gabata bayan dawowarsa daga jinyar wata uku a kasar Birtaniya.

Wasu kungiyoyin kabilu sun rika tayar da kura a ’yan watannin nan, bayan da ’yan kabilar Ibo suka rika kartar kasa suna neman ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara, hakan ya sa wasu kungiyoyin matasan Arewa ba ’yan kabilar Ibo wa’adin zuwa 1 ga Oktoba, su tattara nasu-ya-nasu su bar Arewa, yayin da wasu kungiyoyin yankin Neja-Delta suka fara kiraye-kirayen kafa kasarsu.

Mutanen Najeriya kusan miliyan 180 da Musulmi da Kirista suka fi rinjaye, kuma suka fito daga kabilu 250, galibi dai suna zaune lafiya cudanye da juna.

A jawabin da aka nuna kai-tsaye ta akwatunan talabijin bayan dawowarsa ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ce yana bibiyar abubuwan da suke faruwa a kullum lokacin da yake waje, kuma ya damu da tattaunawar da ake yi kan yiwuwar raba kasar nan. “Na kadu game da wasu kalaman, musamman a kafofin sada zumunta wadanda suka wuce gona da iri ta hanyar nuna rashin amincewa da kasancewarmu dunkulalliyar kasa,” inji Buhari.

Ya kara da cewa: “Bakin alkalami ya riga ya bushe game da batun hadin kan Najeriya, babu batun sake tattaunawa a kai. Don haka kada mu bar wadansu marasa hankali su tado mana fitinar da za su iya gudu su bar wadansunmu da magance ta, kila ma da jininsu.”

Shugaba Buhari ya ce, “miyagun ’yan siyasa ne suke ruruta” wasu daga cikin rikice-rikicen kabilanci a kasar nan.

Shugaba Buhari ya ce ya fi alfanu ga ’yan Najeriya su hada hannu don fuskantar matsalolin tattalin arziki da na tsaro. Ya kuma shaida wa hukumomin tsaro cewa kada su yi sanya game da nasarar da aka samu a kan ’yan Boko Haram a wata 18 da suka gabata, ta yadda hakan “zai jawo sakaci,” inda ya ce wajibi ne Najeriya “ta kara kwazo da zage dantse” a yakin da take yi da ’yan ta’addan.

kurar neman kasar Biyafara da wa’adin da matasan Arewa suka ba Ibo ta tilasta Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ganawa da shugabanni daga sassan kasar a kokarinsa na dakile kurar, wadda ta tunato da irin abin da ya faru a lokacin da kabilar Ibo suka nemi ballewa a 1967 wanda a karshe ya jawo asarar rayukan kimanin mutum miliyan daya.