Likitan kungiyar kwallon kafa ta Ajantina Honoero de Agostino a shekaranjiya Laraba ya gargadi shahararren dan kwallon Ajantina da kuma kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi akan kada ya kuskura ya ce zai buga wasa a tsakanin Real Madrid da na FC Barcelona wanda zai gudana a ranar 21 ga watan nan da muke ciki.
Likitan ya ce akwai hadarin gaske idan Messi ya ce zai buga wannan wasa da ake wa lakabi da El-Classico saboda muhimmancinsa.
Da yawa daga cikin magoya bayan FC Barcelona sun yi murna a ranar Litinin da ta wuce bayan da shugaban kulob din ya bayyana cewa Messi zai dawo wasa ne a ranar 21 ga wannan wata da muke ciki.
Messi dai ya ji ciwo ne tun a ranar 26 ga watan Satumbar wannan shekara a ranar da kulob din Barcelona ya hadu da na Las Palmas a gasar rukunin La-Liga ta Sifen kuma tun daga wancan rana Messi bai sake buga kwallo ba.
Likitan ya ce ganin yadda Messi bai gama warwarewa ba ne ta sa Ajantina ta ki gayyatarsa a wasan neman gurbi na tafiya gasar cin kofin duniya da kasar ta yi da Brazil a jiya Alhamis da kuma wanda za ta kara da Kolombiya a makon gobe.
Akwai alamun da suka nuna Messi zai dawo wasa ne a ranar El-Classico amma Likitan ya nuna shakkunsa a kan haka, inda ya ce idan Messi ya sake samun matsala to babu shakka zai shafe lokaci mai tsawo yana jinya.
Kada Messi ya kuskura ya ce zai buga wasan Madrid da Barcelona – Likitan Ajantina
Likitan kungiyar kwallon kafa ta Ajantina Honoero de Agostino a shekaranjiya Laraba ya gargadi shahararren dan kwallon Ajantina da kuma kulob din FC Barcelona na…