A bana, Shugaba Muhammadu Buhari ba zai karbi baki masu zuwa gaisuwar Sallah ba kamar yadda ya saba.
Mai taimakawa shugaban kasar a kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, wanda ya bayyana hakan ranar Juma’a a wata sanarwa da ya fitar, ya ce hakan wani mataki ne na hana coronavirus yaduwa.
“Shugaban kasar, wanda bisa al’ada yakan yi bikin Sallah tare da manyan jami’an gwamnatida shugabannin siyasa da shugabannin al;umma, da shugabannin addinin Musulunci da na Kirista da yara, ba zai karbi gaisuwar Sallar ba a yunkurin ganin an hana coronavirus ci gaba da yaduwa”, inji shi.
- Buhari ya kai wa majalisa kasafin 2020 da aka yiwa gyara
- Dokar rufe fuska: ‘Buhari bai saba doka ba’
Malam Garba Shehu ya kuma ce Shugaba Buhari zai yi Sallar Idi ne a gida don martaba dokar da hukumomin Yankin Babban Birnin Tarayya suka kafa ta rufe wuraren ibada da nufin “ceton rayukan jama’a da kuma kare su daga hadari”.
Bugu da kari, inji Malam Garba Shehu, shugaban kasar ya yanke shawarar yin Sallar Idi a gida ne don biyayya ga umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar na dakatar da Sallar Idi.
“Haka kuma [wannan mataki] ya dace da bin umarnin Sarkin kuma Babban Shugaban kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III na dakatar da Sallar Idi a cikin jam’i a fadin kasa, da kuma dokar hana taruwar jama’a ta Kwamitin Shugaban Kasa mai Yaki da COVID-19”, inji sanarwar.