Gwamna Babagana Umara Zulum, ya ce kada a debe tsammani a kan sauran ’yan matan Chibok da mayakan Boko Haram suka sace shekaru bakwai da suka gabata.
Cikin sakonsa na kyautata zato da karfafar gwiwa gami da rarrashin iyayen mata da kuma ’yan uwansu a ranar Laraba, Gwamna ya ce za a ceto sauran ’yan matan Chibok da ma sauran mutanen da aka sace a Jihar cikin koshin lafiya.
A sakon nasa na cikar shekaru bakwai da sace daliban, Zulum ya bayyana cewa damuwar iyayen matan damuwarsa ce kasancewarsa uba ga dukkan ’ya’ya a Jihar Borno.
“A matsayi na uba, ina jin takaici da kuncin da iyayen ke ciki tsawon shekara bakwai yaransu na hannun ’yan ta’adda.
“Ina kira ga iyaye, musamman wadanda suka haifi ’ya mace, da su dakata na wani takaitaccen lokaci domin su yi tunani a kan halin da iyayen wadannan dalibai ke ciki da sanin cewa an dauke musu ’ya’yansu fiye da tsawon kwanaki 2,549.
“A yi nazari da tunani a kan yadda iyaye da dangin wadannan ’yuan mata suka kasance cikin kowane dare da yini da suka shude.
“Tabbas babu wata azabtarwa da tashin hankali mafi muni da ta kai rashin sanin makomar da ’ya’yansu ke ciki a hannun mayakan Boko Haram.
“Babu iyayen da za su iya debe tsammani a kan ’ya’yansu da suka bace, saboda haka a kullum fatansu na zuwa ne tare da fargaba da dimuwa mai tsananin gaske.”
“Haka kuma, a ganawar da na rika yi da Shugaba Muhammadu Buhari, na lura cewa akwai damuwar ’yan matan a tattare da shi kamar yadda ta kasance ga mu da kuma iyayensu.
“Sau tari shugaban kasar ya nuna min cewa ba zai debe tsammani a kan ceto ’yan matan ba, wanda ya ce duk da cewa an sako wasu daga cikinsu kuma Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da ba su duk wata kula da dawainiya da su, ba zai iya samun kwanciyar hankali ba har sai ragowar sun kubuta.
“Da wannan nake kiran al’umma su taimaka da addu’o’i ga wadanda aka sace da kuma fatan dawowar zaman lafiya mai dorewa a Jihar Borno.
“Ina rokon Allah cikin RahamarSa marar iyaka, ya amsa addu’o’inmu kuma ya bamu zaman lafiyar da muke dokin samu tsawon shekaru 12 da suka gabata,” in ji Zulum.
Ya kuma nemi a ci gaba da goyon bayan jami’an tsaro da tallafa wa masu bayar da agaji domin fatan da ake yi na samun zaman lafiya ya tabbata.
Duk da cewa wasu daga cikin daliban 276 da aka mayakan Boko Haram suka sace a garin Chibok da ke Borno, sai dai har yanzu akwai 112 da har yanzu ba a iya gano su ba, kuma iyayensu na fatan ganin ’ya’yansu kafin su bar duniya.