✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada a shiriritar da farfado da noman alkama da shinkafa

A ranar Talatar makon da ya gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bikin kaddamar da shirin noman ranin bana, a kauyen Zauro da ke…

A ranar Talatar makon da ya gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bikin kaddamar da shirin noman ranin bana, a kauyen Zauro da ke cikin karamar Hukumar Birnin Kebbi ta Jihar Kebbi, shirin da ake da aniyar mayar da hankali akan noma alkama da shinkafa a wasu jihohi 9, da gwamnatin tarayyar ta zaba don wannan gagarumin shiri mai matukar muhimmancin gaske, akan wadata kasar nan da abinci da kuma farfado da tattalin arzikin kasar da uwa uba samar da ayyukan yi ga dimbin miliyoyin matasan kasar nan. A lokacin da ya ke kaddamar da shirin Shugaba Buhari, ya nemi Gwamnonin Jihohin Arewa da lallai su tashi tsaye wajen ganin sun taimaka wa manomansu, wajen ganin suna yin noma rani da damina.
Shugaba Buhari, wanda ya mika cekin kudi na N2.6miliyan ga Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, a zaman rancen da za a raba wa manoman ranin na alkama da shinkafa na jihar, ya jaddada muhimmancin da ayyukan gona suke da su wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan, baya ga samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa, zai kuma kawo karshen zaman kashe wando, tare da wadata mutanen kasar nan da abincin da za su ci, musamman a irin wannan lokaci da farashin danyen man fetur da ya ke samar da sama da kashi 75 cikin 100  na kudin shigar kasar nan ya fadi warwas. Dadin dadawa in ji shugaban kasar, habaka ayyukan gona da samar da ayyukan yi da kawo karshen rashin zaman lafiyar da kasar nan take fama da su na cikin alkawurran da jam`iyyarsu ta APC ta yi wa `yan kasa a lokacin yakin neman zabenta. Wadancan kudi Naira biliyan 2.6,da aka ba manoman Jihar Kebbi na cikin Naira biliyan 40 da Babban Bankin kasa ya tsakuro daga cikin Naira biliyan 220 da ya kebe don bayarwa bashi akan habaka ayyukan gona ga manoman kasar nan, akan kudin ruwan da ba su wuce kashi 9 ciki 100, ba kamar yadda Gwamnan Babban Bankin Mista Godwn Emefiele, ya fadi a wajen bikin na Jihar Kebbi.l
 Shi ma Gwamnan Jihar Kebbi, kuma mai masaukin baki da jiharsa ke cikin jihohi irin su Zamfara da Adamawa da Jigawa da Taraba  da Ebonyi da Gwambe da za su cii gajiyar shirin nomanalkama da shinkafar,Sanata Bagudu ya sha alwashin yin dukkan abinda ya wajaba, wajen ganin wanna shiri ya kai ga nasara. Har ya kara da ba da tabbacin cewa jiharsa kadai za ta iya noma kashi 50 zuwa 60  cikin 100  na shinkafar da kasar nan t ke bukata, ya yin da ya sha wani alwashin na cewa nan da shekaru uku  zuwa hudu, manoman jiharsa za su iya samar da kashi 20 cikin 100, na alkamar da kasar nan take bukata. Gwamna Sanata Bagudu ya fadi haka ne a cikin makon jiya a lokacin da yake karbar bakuncin Manajin Daraktan Bankin Access, da ya kai masa ziyarar ban girma a Birnin Kebbi Hedkwatar jihar, inda gwamnan ya kara da cewa tuni ya samu tabbaci daga Kamfanonin yin Fulawa na kasar nan a kan za su sayi dukkan rarar alkamar da manoman ka noma kuma akan ingantaccen farashi.
Tun bayan da Shugaba Buhari ya nada shahararren masanin aikin gonar nan Mista Audu Ogbeh, a matsayin Minstan Ayyukan gonada raya karkara, da kuma jin aniyar da wannan gwamnatin take da ita na ba fannin ayyukan gonar muhimmanci da ya kamata, manoma daban-daban da kungiyoyinsu da masana tattalin arzikin kasa da na fannin noman, suke ta tofa ta albarkacin bakunansu akan irin hanyoyi da matakan da suke  ganin ya kamata mahukunta su dauka don kwalliya ta biya kudin sabulu, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu, kuma shirin ya dore.
Masu irin wannan tunani, suna ganin lallai akwai bukatar samar da ingantattun kuma wadatattun iri da takin zamani da magungunan kwari da farin dango, a lokacin da ya dace, sai kuma wadata manoman da Malaman gona da za su rinka nusantar da su dabarun noma irin na zamani. Su kuma ce manoman kasar nan a yau ba sai gobe ba, suna matukar bukatar samun kasuwa da ingantaccen farashi akan dukkan amfanin gonar da suka noma adaidai kakar kowane amfanin gonar. Na`urorin noma irin na zamani su ma manoman kasar nan na tsananin bukatarsu, musamman matsakaita da kananan manoma, haka labarin yake akan samar da basussuka masu saukin kudin ruwa da kuma saukin biya. Akwai kuma bukatar samar da hanyoyin karkara da ma na cikin birane, ta yadda fito da amfanin gonar zuwa kasuwanni da masana`tun da za a rinka sarrafa su, za su zama cikin sauki. Su ma masu masana`antun da suke sarrafa amfanin gona (kamar su shinkafa da alkama da da rogo da dawa da sauransu) ya zama wajibi gwamnatin tarayya da na jihohi su rinka tilasta musu suna shiga harkokin noma dukkan irin amfanin gonar da suke sarrafawa, ta hanyar share musu ko basu filayen noman da suke bukata, su ma sauran manoman kasa su na da bukatar kara samun gonakin da za su noma daga Mahukuntansu
A tsakiyar watan jiya an ruwaito gwamnan jihar Zamfara kuma Shugaban kugiyar Gwamnonin kasar nan, Alhaji Abdulazeez Yari yana fada wa manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan wani taro da gwamnonin suka yi da Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, cewa taron da suka yi ya mayar da hankali ne akan yadda za a iya noma wadatacciyar shinkafar da kasar nan ta ke bukata nan da shekaru biyu, ta yadda za a haramta shigo da ita kwata-kwata. Gwamna Yari, ya ce a wannan karon babu abin da zai sanya kasar nan ta kasa cimma wannan buri don kuwa akwai jajircewa daga shugabannin wannan lokacin.
Tunda dai yanzu mahukuntan kasar nan ra`ai-ra`ai sun ga irin annobar da faduwar farashin danyen man fetur ta jazawa tattalin arzikin kasar nan, annobar da suka rinka dauka tamfar busa, duk kuwa da irin gargadin da hannunka mai sanda da masana tattalin arziki su ka dade suna yi wa mahukuntan, cewa arzikin man fetur ba mai dorewa ba ne. Don haka ba abin dogaro ba ne, aikin gona shi ne mai dorewa, kuma abin dogaro, don haka ina fata a wannan karon mahukuntan da gaske suke akan wannan yunkuri da suka yi. A nan Ina fatan  Allah Ya sanya kada su shiriritar da shirin na farfado da noman na alkama da shinkafa da dukkan shirye-shiryen da suka bullo da su nan gaba da sunan ganin ingantuwar harkokin ayyukan noma da kiwo, kamar yadda sauran shirye-shiyen bunkasa fannin irin su shirin “Wadata kasa da Abinci” na OFN da na “Juyin juya hali akan  aikin noma” wato GR da na Noma Alkama tan miliyan daya da gwamnatin mulkin soja ta jihar Kano ta yi a shekarun 1980. Dukkan wadannan shirye-shirye ba wanda ya kai bentansa, saboda rashin samun kulawar gwamnatocin da suka kirkiro shirin. Ko a wannan mulkin farar hular, a shekarar 2005, shugaba Obasanjo ya bullo da shirin farfado da noman shinkafa. Marigayi shugaba Umaru Musa `Yar`aduwa, har shatawa ya yi a lokacin, cewa zuwa wannan shekarar ta 2015, kasar nan za ta daina shigo da shinkafa. Amma mai karatu dubi inda muke a yau ana kashe Dala biliyan biyu duk shekara wajen shigo da shinkafa.