Naira biliyan 37 da aka sanya a cikin kasafin kudin bana wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a makon jiya domin gyara Majalisar Dokoki ta Kasa, ba komai ba ne illa barnar kudi da almundahana sannan kwata-kwata ba ya kan tsari lura da halin da ake ciki.
Ranar Litinin din makon jiya aka fitar da bayanin yadda za a kashe kudaden ta bakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan. Ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu ne a kan dokar aikin gyaran majalisar bayan da ’yan majalisar suka tattauna da shi kan mawuyacin hali da ginin majalisar ke ciki.
Kudin da aka ware domin gyara majalisar ba ya daga cikin Naira biliyan 128 da aka ware a kasafin kudin majalisar na badi. Wani abin mamaki kuma shi ne Naira biliyan 37 da za a kashe wajen gyaran majalisar za a dauko su ne daga cikin kasafin kudin Birnin Tarayya Abuja (FCDA) wanda kudin da aka ware domin ayyukan ci gaban birnin Naira biliyan 62.4 ne, kuma wannan yana nuna cewa sama da rabin kasafin kudin FCDA domin ayyuka masu muhimmanci za su zirare wajen gyara ginin Majalisar Dokoki ta Kasa kacal. Shugaban Majalisar Dattawan ya yi kokarin ya fayyace aikin gyaran majalisar inda yake cewa babu wani gyaran a-zo-a-gani da aka yi a majalisar tsawon shekara 20 saboda haka wani bangare na ginin majalisar ya lalace. Saboda haka babu wasu kudi da aka ware domin gyaran majalisar, Majalisar dai ta karbi kudade masu yawa domin a habaka ta tun cikin 1999. A shekarar 2013, Bangaren Zartarwa (FEC) ya amince a kashe Naira biliyan 40.2 kan kwangilar gina kashi na uku na bangaren ginin majalisar (Phase lll ) da kuma daga darajar ginin majalisun biyu.
Haka a shekarar 2017 Majalisar Dattawa ta yi kasafin Naira biliyan 1.25 domin sayen kayayyakin kula da harkar tsaron majalisar. Baya ga wancan kudi, Majalisar ta ware Naira miliyan 440 domin sayen irin wadancan kayayyaki na kula da harkar tsaro ga ofisoshin majalisar. Mafi kololuwar almundahanar da aka yi a tsakanin Majalisa ta Takwas da tsohuwar Ministar Kudi, Kemi Adeosun, shi ne na kashe Naira miliyan 454 domin sayen kayayyakin ofisoshin majalisar da kuma wasu Naira miliyan 109 su kuma an kashe su ne domin sayen kayan kula da sadarwa (ICT) a cikin majalisar. Gaskiyar lamari shi ne Majalisar Dokokin tana kashe makudan kudi a kan ayyuka marasa muhimmanci wadanda ba za su amfani talakan Najeriya ba.
Haka zalika muhawara ta barke tsakanin ’yan kasa a kan wannan makudan kudi da aka ware domin gyaran ginin Majalisar Dokoki ta Kasa. Kudin da aka ware domin gyaran majalisa har Naira biliyan 37 su haura wadanda aka ware domin gyaran hanyoyin da suke cikin Najeriya, misali an ware Naira biliyan 36.6 ne kacal domin gyara manyan hanyoyin da suke cikin kasar nan ga Hukumar Kula da Hanyoyin Tarayya (FERMA) domin ta gyara hanyoyin Gwamnatin Tarayya a fadin Najeriya.
Babu dalilin da Gwamnatin Tarayya za ta kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 37 domin gyaran ginin Majalisar Dokoki ta Kasa, alhali ita kanta gwamnatin tana kukan rashin kudi wajen biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatanta. Kuskure ne, sannan ana fifita abin da ba ya da muhimmanci a kan mai muhimmanci, Kasar da aka ayyanata a matsayin hedkwatar talauci ta duniya, sannan a kashe wadannan makudan kudi wajen gyaran ginin majalisa, alhali ga asibitoci da hanyoyi duk sun lalace suna cikin halin kunci, wannan yana nuna yadda ’yan majalisa suke nuna halin ko-in-kula da nuna rashin tausayin ’yan Najeriya.
Kasar da take fafutika wajen farfado da tattalin arzikinta bayan masassarar da ya yi fama da ita. Makudan kudi irin wadannan kamata ya yi a kashe su wajen manyan ayyuka da na walwalar jama’a domin habaka tattalin arziki, ba wai a rika kashe kudade wajen gyaran ofisoshin ’yan majalisa ba, wadanda yawansu sanatoci bai wuce 109 da wakilai 360 ba. Don haka Shugaba Buhari ya umarci bangaren kudi domin sanya wadannan kudade wajen inganta lafiya da ilimi. Dalili kuwa shi ne ana samun habakar tattalin arziki ne kawai idan ’yan kasa suna da ingantaccen ilimi da kuma lafiya.
Tana yiwuwa Shugaba Buhari ya sa hanu a kan wannan kasafi kudin gyaran ginin Majalisa ne lura da biyayya da goyon bayan da wannan majalisa take ba shi a dukkan matakai. Idan wannan ita ce hanyar da za a saka wa wadanda suka yi irin wannan biyayya, to babu makawa wannan shi ne fifita abu marar muhimmanci a kan wanda ya fi muhimmanci, kuma wannan shi zai ci gaba da jawo tabarbarewar tattalin arzikin kasa da kuma al’umma.