✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kabeji mai nama

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya bamu ikon tarbiyantar da su yadda yakamata.  A yau na kawo muku…

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya bamu ikon tarbiyantar da su yadda yakamata.  A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama amma yawaita girka abinci iri daya na ginsan yara da kuma maigida. A kullum mutum yana son cin sabon abu. Don haka dole ne mata a dage wajen koyan nau’ukan girke-girke domin kayatar da abincin da ake dafawa a gida.

Abubuwan da ake bukata

Nikakken nama

Kabeji

Attarugu

Koren tattasai

Albasa

Magi

Karas

Kori

Citta

Tafarnuwa

Man gyada

Hadi

A wanke nama sannan a markada shi a na’urar nika nama a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta da gishiri kadan sannan a samu kabeji a bare shi manya-manya a tafasa da gishiri kadan na tsawon mintuna biyar. Sannan a tsame a ajiye a gefe.

A dora tukunya a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da nikakken nama a zuba magi da kori da garin citta da tafarnuwa da jajjagen attarugu da yankakken koren tattasai ayi ta gaurayawa har sai naman ya  soyu sannan  a kwashe.

A samu kabejin da aka tafasa sannan a shimfida shi kamar tabarma sannan a debo hadin nama a zuba a ciki sannan ayi masa nadin tabarma a tottoshe gefe-gefen.

Sannan a dora tukunya a wuta a zuba man gyada kadan ba mai yawa ba, sannan a zuba wannan ninkin kabejin a cikin man a soya sama-sama sannan a kwashe.

Za a iya cin wannan hadin kabejin da shayi mai zafi da safe a matsayin abun karyawa.