Jam’iyyar APC mai mulki ta yi raddi ga dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kan zanga-zangar da ya jagoranci wasu jiga-jigan jam’iyyar wajen neman soke zaben shugaban kasa da aka gudanar.
A martaninsa, Daraktan Yada Labarai na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC, Bayo Onanuga, ya ce ya kamata Atiku ya martaba shekarunsa da kuma ofishin mataimakin shugaban kasa da ya taba rikewa a baya.
- Bayan shekara 10, Buni ya soke haramcin hawa babur a Gabashin Yobe
- Soja ya harbe abokin aikinsa, ya kashe kansa a Sakkwato
Martanin na APC na zuwa ne bayan da Atiku ya gudanar da zanga-zangar neman a soke zaben shugaban kasa da na ’yan majalisar tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Onanuga, ya ce “Mun dauka cewar kamar yadda Atiku ya ce zai tafi kotu neman hakkinsa, can zai je, amma sai ya bige da bin tituna yana zanga-zanga.
“Abin da muka gani daga Atiku a yau (Litinin) ba komai ba ne face zafin faduwa zabe.
“Muna shawartar sa da ya nemi lauyoyi ya nufi kotu, amma bin tituna da sunan tara mutane don yin zanga-zanga ba nashi ba me,” in ji Onanuga.
Ya kara da cewar kamata ya yi Atiku da jam’iyyarsa su zauna don tara hujojjin da suka ce suna da su don tunkarar kotu da su.
Tun da fari dai Atiku na jam’iyyar PDP ya bukaci a soke zaben shugaban kasa kan zargin kura-kurai da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi a yayin zaben.
Atiku dai ya zo na biyu a zaben shugaban kasa da aka gudanar, bayan shan kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.