A wani yanayi mai kama da na juyin mulki, sojojin Burkina Faso sun tsare Shugaban Kasar, Roch Marc Christian Kabore, saboda yadda jami’an tsaron kasar suka ce gwamnatinsa ba ta taimaka musu ba lokacin da suke yaki da ’yan tawaye.
Labarin dai na zuwa ne ranar Litinin, kwana daya bayan sojojin sun fara tayar da kayar baya a barikokin sojin kasar daban-daban.
- Za mu bi diddigin kisan da aka yi wa Hanifa —Shekarau
- Matasa sun kone makarantar da aka binne Hanifa
Daga bisani dai ranar Lahadi, an jiyo karar harbe-harbe a kusa da gidan Shugaban da ke babban birnin kasar na Ouagadougou.
Gidan Talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa an hangi motocin silke da dama daga tawagar Shugaban Kasar da alamun harsasan harbi a jikinsu, wata ma har da fallatsin jini a jikinta.
Wasu majiyoyi dai sun ce shugaban na can a tsare a wani sansanin sojoji.
Ya zuwa yanzu dai babu wani martani daga Fadar Gwamnatin Kasar, wacce ko a ranar Lahadi sai da ta musanta jita-jitar yiwuwar yin juyin mulkin.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito cewa an tsare Shugaban ne tare da wasu mukarraban gwamnatinsa.
Shugaba Kabore ya fara jagorantar Burkina Faso ne tun shekarar 2015 bayan wata tayar da kayar baya da ta hambarar da gwamnatin Shugaba Blaise Campaore, wanda ya shafe kusan shekara 30 a kan mulki.
An dai sake zabar Kabore a watan Nuwamban 2020 domin sabon wa’adin mulkin shakara biyar, amma ana ci gaba da sukar lamirin gwamnatinsa kan karuwar tashe-tashen hankula a kasar.