Shugaban rikon kwaryar kasar Mali Bah Ndaw da Fira Minista Moctar Ouane sun ajiye mukamansu.
Kamfanin dillacin labaran kasar Faransa (AFP) ne ya ruwaito hakan a ranar Laraba, ta majiyoyin sojin kasar da na diflomasiyya.
A yammacin Litinin sojojin Mali suka kama shugaban rikon kwaryar kasar da fira ministan kasar, tare da tsare su a barikin sojoji na Kati da ke kusa da Bamako babban birnin kasar.
A sansanin sojin ne ake zargin sojojin sun yi wa rayuwar shugabannin biyu barazana har ta kai ga sun ajiye mukamansu.
Sai dai mataimakin shugaban kasar na rikon kwarya, Assimi Goita, ya ce an fattaki su sakamakon keta dokar mika mulkin kasar.