Juventus ta tsawaita kwataragin dan wasan bayanta Giorgio Chiellini da shekaru biyu kamar yadda kungiyar ta sanar a makon nan.
Hakan na zuwa ne bayan ’yan makonni da wasan ya taimaka wa tawagar kwallon kafa ta Kasar Italiya lashe gasar cin Kofin Nahiyyar Turai ta Euro 2020.
- An dawo wa dakin karatu littafin da aka ara shekara 63 da suka gabata
- Mata ta sheka wa mijinta tafasasshen ruwa a Kano
Tun a karshen watan Yuni kwataragin dan wasan mai shekara 36 ya kare a kungiyar mai buga gasar Serie A ta Italiya.
A yanzu dan wasan ya rattaba hannu kan kwantaragin da zai dauke shi ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2023, sabanin jita-jitar da aka rika yadawa baya ta cewa kwantaragin zai kare a shekarar 2022.
A shekarar 2005 ce Chiellini ya koma Juventus daga Roma, kuma ya kasance kashin bayan kungiyar tun daga wannan lokaci da kawo yanzu ta lashe kofin Serie A 9 a jere, inda Inter Milan da taka musu birki a kakar da ta gabata.