✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juventus ta sallami kocinta Massimiliano Allegri

A ranar Laraba ce Juventus ta doke Atalanta 1-0 a birnin Rome a wasan karshe na Coppa Italia.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da kocinta Massimiliano Allegri a wannan Juma’ar.

Sallamar kocin na zuwa ne kwana biyu bayan ya jagoranci ’yan wasanta sun lashe kofin gasar Coppa Italia.

Juventus ta ce ta sallani kocin mai shekaru 56 saboda saba wa ɗabi’unta da ya yi yayin wasan da kungiyar ta yi nasara a kan Atalanta.

A ranar Laraba ce Juventus ta doke Atalanta 1-0 a birnin Rome, amma an bai wa Allegri jan kati saboda hayagaga da ya yi wa alƙalan wasa.

Tuni mahukuntan gasar ƙwallon Italiya suka ƙaddamar da bincike a kan Mista Allegri tare da dakatar da shi wasanni biyu.

Allegri, wanda ya lashe kofuna 12 a zama karo biyu da ya yi a Juventus a matsayin koci, ana kuma zarginsa da cakuma tare da yi wa babban editan jaridar Tuttosport barazana a wani taron manema labarai da aka gudanar bayan wasan.

“Korar ta biyo bayan wasu ɗabi’u a lokacin da kuma bayan tashi daga wasan Coppa Italia wanda kulob ɗin ke ganin sun saɓa da al’adun Juventus,” a cewar sanarwar da kulob ɗin ya fitar.

Nasarar lashe kofin a ranar Laraba ta sa Allegri ya kafa tarihin cin kofin har sau biyar a matsayin mai horarwa.

Juventus wadda ke matsayi na hudu a teburin Serie A da maki 25 tsakaninta da Inter Milan mai rike da kofin, ta samu maki 15 ne kacal a cikin wasanni 15 na bayan nan da ta yi a gasar.

A ranar Litinin da daddare ne za ta fafata da Bologna, inda tuni kungiyoyin biyu suka samu tikitin shiga Gasar Kofin Zakarun Turai na kakar wasa mai zuwa.