✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Joseph Yobo ya gamu da fushin surukansa

Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Norwich City da ke Ingila ya gamu da fushin surukansa bayan sun…

Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Norwich City da ke Ingila ya gamu da fushin surukansa bayan sun aika masa sako na musamman cewa ya dawo gida a daura masa aure da ’yarsu mai suna Adaeze a gargajiyance idan ba haka ba za su dauki mataki a kansa, kamar yadda wata Mujalla da ake kira Yes ta kalato a karshen makon jiya.
Ita dai mai dakin Yobo da ta fito daga kauyen Iru-Owelle da ke karamar Hukumar Idemili ta Kudu a Jihar Anambra, iyayenta sun bayyana bacin ransu ne akan rashin daura musu aure a gargajiyance tun bayan an daura aurensu a Coci shekara da shekaru.
“Yobo bai auri ’yarmu a gargajiyance ba kamar yadda al’adarmu ta bukata don haka ne muke nuna bakin cikinmu a kan haka. Al’adarmu ta Igba Nkwu ta nuna duk wanda ya auri mace a yankinmu ba tare da an kara da na gargajiya ba tamkar ba aure ya yi ba, don haka muke rokonsa ya dawo gida don a sake daura aurensu a gargajiyance”, inji surukan Yobo a lokacin da suke hira da wakiliyar Mujallar Yes.
“A gaskiya muna mutunta Joseph Yobo musamman kasancewarsa shahararren dan kwallo, kuma mun yi murna da ya zama daya daga cikin surukinmu don haka hore shi ya mutunta al’adarmu a matsayinsa na surukinmu wajen dawowa kauyenmu a sake daura aurensu da diyarmu Adaeze a gargajiyance.”
“Idan za ku tuna, Marigayi Ojukwu sai da ya koma kauyensu mai suna Ngwo da ke Enugu aka sake daura aurensa da Bianca a gargajiyance duk da irin shagulgulan bikin da aka yi a aurensa da Bianca a Abuja. Don haka dukiyar da Yobo ya kashe a auransa a zamance bai isa ba hatta sai ya koma kauye na yi na gargajiya idan yana son auren nasu ya yi albarka”.