✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Kashe Shugaban ’Yan Sanda A Tarzomar Tsadar Mai A Jordan

Mutum 44 sun shiga hannu bayan an harbe wani babban hafsan dan sanda har lahira a tarzomar da ta barke kan tsadar man fetur a…

Mutum 44 sun shiga hannu bayan an harbe wani babban hafsan dan sanda har lahira a tarzomar da ta barke kan tsadar man fetur a kasar Jordan.

Gwamnatin kasar ta ce an harbe Mataimakin Shugaban ’Yan Sandan Lardin Maan, Kanar Abdul Razzaq Dalabeh, har lahira ne a yayin da yake aikin shawo kan masu zanga-zangar a garin Al-Hussainiya.

A ranar Juma’a Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar Jordan, Mazen Al-Faraya, ya ce, “Hukumomin tsaro na aiki domin kamo wanda ya harbi Kanar Abdul Razzaq a ka, domin ya girbi abin daya shuka.”

Hukumar Tsaron Al’ummar Jordan ta ce, masu tarzomar sun ji wa wasu ’yan sanda biyu rauni a yankin na Al-Hussainiya, kuma “Mutum 44 daga cikin masu tarzomar sun shiga hannu a larduna daban-daban kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.”

Sanarwar ta ce an tura karin jami’an tsaro a yankunan da aka samu hatsaniyar, wadda “bata-gari” ke neman yin amfani da ita domin biyan bukatunsu.

A ranar Juma’a, Sarki Abdullah II na kasar Jordan ya sanar cewa “Duk wanda ya dauki makami a kan gwamnati zai yaba wa aya zaki.”

Tsadar mai a Jordan

A makon jiya ne direbobin tasi da manyan motoci suka fara yajin aiki kan tsadar mai a Jordan, kafin a ranar Larabar wannan makon, ’yan kasuwa da direbobin bas-bas suka bi sawu.

A makon nan ne dai aka fara zanga-zanga a sassan kasar inda dandazon mutane suka toshe hanyoyi suna kona tayoyi, har a wasu wuraren suka takali jami’an tsaro.

A halin yanzu farashin mai, musamman dizel da kananzir, wadanda ake amfani da su wajen girki da manyan motoci ya kusa ninkawa a kasar, idan aka kwatanta da yadda farashin yake a farkon shekarar nan.

Gwamnatin kasar ta gabatar da wasu matakai da take neman dauka kan matsalar, ciki har da bayar da tallafi ga iyalai masu karamin karfi.