✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jonathan ya taya Tinubu da Atiku murnar zama ’yan takara

Jonathan ya jinjina wa Kwankwaso da Peter Obi da sauran masu neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023

Toshon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya taya Bola Tinubu murnar zama dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulki.

Jonathan wanda a yi ta cece-ku-ce kan yiwuwar fitowarsa neman takarar shugaban kasa a APC ya kuma taya tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, murnar samun tikitin takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.

“Hakika nasarar da kuka samu a zaben fidda gwani na jam’iyyunku bayan kun gabatar da kanku ga zabubbukan masu tsauri da tsarin zabe yana nuna imaninku da sha’awarku ga ci gaban al’ummarmu,” inji shi.

Ya taya ’yan takarar shugaban kasar manyan jam’iyyun siyasar Najeriya murna ne a sakon da ya fitar a ranar Juma’a ta shafinsa na Twitter.

A cewarsar, “Yayin da kuke ci gaba da yakin neman zabe, yana da kyau al’amuran da suka addabi kasar nan da ingantattun hanyoyin magance su su dauki matakin farko.

“Ina kira gare ku da ku gudanar da yakin neman zabenku ba tare da nuna son kai, raba kan jama’a da ha’inci ba, ta yadda a karshe Najeriya za ta yi nasara, dimokuradiyya za ta yi nasara, haka rayuwa za ta inganta.”

Sakon nasa ya fara ne da cewa, “Ina taya wadanda suka samu nasara a zabukan fidda gwani a fagen siyasa, musamman Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Peter Obi na Jam’iyyaram’iyyar Leba, da Asiwaju Bola Tinubu na Jam’iyyar APC.

“Haka kuma, da jiga-jigan wasu jam’iyyun da su ma suka kammala zaben fidda gwanin da suka hada da Sanata Rabi’u Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da Malik Ado-Ibrahim na YPP da Cif Dan Nwanyanwu na ZLP da Dumebi Kachikwu na ADC da kuma Adewole Adebayo na jam’iyyar SDP.”