✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Kungiyar Fulani’ ta saya wa Jonathan fom din takarar Shugaban Kasa a APC

Wasu gwamnonin Arewa masu kusanci da Shugaba Buhari ne kan gaba wajen saya wa Jonathan fom din takarar shugaban kasa a Jam'iyyar APC mai mulki

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya sayi fom din takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC.

A ranar Litinin ne wata kungiya mai suna ’Kungiyar Fulani’  ta sayi fom din a Abuja a madadin Jonathan wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, don ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Kawo yanzu dai tsohon shugaban kasar bai fito ya bayyana sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba.

Wasu majiyoyi masu tushe sun shaida wa wakilinmu cewa wasu gwamnoni biyu a jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya ne kan gaba a yunkurin na ganin Jonathan ya zama magajin Shugaba Buhari a 2023.

Daya daga cikin gwamnonin, wanda a baya-bayan nan suke uwa suke makarbiya a APC, ya fito ne daga yankin Arewa ta Gabas, dayan kuma daga Arewa maso Yamma.

Majiyar ta ce kowanne daga cikin gwamnonin biyu na hannun daman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne.

2023: APC na kokarin sulhu

Kwararan majiyoyi sun nuna jam’iyyar APC mai mulki na kokarin fitar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 ta hanyar sasanci.

Jam’iyyar na wannan yunkuri ne ganin yadda yawan mambobinta da ke sayen fom din neman kujerar shugaban kasar ke ta karuwa.

Duk da tsadar fom din da ake sayarwa a kan Naira miliyan 100, kawo yanzu akalla mutum 27 ne suka saya domin zawarcin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ta APC, wadda ke shigin gudanar da zaben fitar da dan takararta na shugaban kasa daga ranar 30 ga watan Mayun da muke ciki zuwa ranar 1 ga watan Yuni.

Majiyoyin masu tushe a jam’iyyar sun ce a halin yanzu was kusoshin jam’iyyar na kokarin lallashin wasu daga cikin masu neman kujerar da su hakura, a samu sasanci.

Wata kwakkwarar majiya a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ya gabatar wa wakilinmu kwafin takardar “Form 18” da jam’iyyar ta tanada domin wadanda za su janye takarar tasu za su cike , a matsayin shaida.

Ta bayyana cewa jam’iyyar ta umarci wasu daga cikin masu neman takarar da su cike fom din su hada da fom dinsu na neman takara, sannan su mayar wa Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Aminiya ta kuma gano cewa jam’iyyar ta bayyana musu cewa za a yi hakan ne a gaban kwamishinan daukar rantsuwa.

Majiyarmu ta ce yin hakan a gaban kwamishian rantsuwar zai hana yiwuwar janye maganar ko zuwa kotu daga baya, idan wani daga cikin wadanda batun janyewar ta shafa ya sauya shawara ya je kotu.

Wani babban jigo a APC, Cif Sam Nkire, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa yin sulhu shi ma halastaccen tsari ne na fitar da dan takara, kuma ya kamata a mutunta hakan idan jam’iyyar ta zabi yin hakan.