Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta ce tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan na da cikakken ’yancin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwarta a babban zabe mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus, ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai ranar Alhamis a birnin Abuja.
- Buhari ya taya shugaban Ghana Akufo-Addo murnar lashe zabe
- An killace Buratai bayan COVID-19 ta kashe Janar din soja
- An kama mutum 2 da suka yi garkuwa da ba’Amurke a jihar Sakkwato
Secondus ya ce har kawo yanzu jam’iyyar ba ta yanke shawara ba dangane da tafarkin tsayar da dan takara da za ta bi, inda a halin yanzu ta ke ci gaba da dakon rahoton kwamitin da ke nazari kan sakamakon babban zaben 2019.
Secondus ya ce jam’iyyar na tsimayen rahoton kwamitin da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ke jagoranta wanda ke nazari kan yadda ta kasance a zaben na 2019 domin gano sabubban da suka sa jam’iyyar ta sha kaye a wancan lokaci.
Da wannan ne Secondus ya kafa hujjar ya sanya ya zuwa yanzu jam’iyyar ba ta yanke hukunci ba dangane da tsarin karba-karba ko yankin da ake sa ran dan takarar zaben shekarer 2023 zai fito.
Aminiya ta ruwaito cewa jam’iyyar PDP ta ce ziyarar da wasu gwamnonin APC suka kai wa Mista Jonathan makonni kadan da suka gabata ta nuna amincewarsu karara kan gazawar APC.
Baya da kura
Ziyarar da gwamnonin suka kai wa tsohon Shugaban Kasar ta bar baya da kura, inda wasu a PDP ke ganin ta a matsayin yunkurin janyo tsohon shugaban kasar zuwa APC mai mulki.
PDP ta bakin Sakataren Watsa Labaranta na kasa Kola Ologbondiyan ta ce ziyarar ba komai ba ce face nuna gazawar APC da kuma kokarin zawarcin tsohon Shugaban Kasar a yayin da babban zaben kasa na 2023 ya gabato.
Gwamnonin da suka ziyarci tsohon Shugaban Kasar a tawagar da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya jagoranta sun hada da Gwamnan Ebonyi, David Umahi, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, da Atiku Bagudu na Kebbi, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, da kuma Abubakar Badaru na Jigawa.
Akwai kuma Kashim Ibrahim-Imam, tsohon wakilin Shugaban Kasa a kan harkokin da suka shafi Majalisar Dokoki ta Kasa.