Domin mu fahimci inda aka fito bari mu koma baya cikin tarihi, mu ga shin haka ake yi a wasu sassa na duniya dangane da siyasa da tsarin dimokuradiyya ko kuwa dai mu ne muke wa kanmu wuji-wuji ina gabas, amma mu kare muna kallon sama a matsayin gabas din?
Bari in soma da misalai guda biyu kawai na yadda siyasa da tsarin dimokuradiyya ke wakana a wasu kasashe, ciki har da wadanda muka ko muke kwaikwayo a tamu tafiyar. Kila bisa wannan fasali mu amince tamu siyasar, ba siyasa ba ce, sayayya ce da rana kiri-kiri.
Tsarin siyasa da gudanar al’amurran dimokuradiyya a ko’ina ya samu tsayuwa da gudanawa, abubuwa biyu ne suka assasa da tabbatar da shi. Na farko tsarin jam’iyya da mutanen da ke shiga cikin jam’iyyar. Na biyu kuwa fasalce-fasalcen tsarin shugabancin jami’iyyar da tsaren-tsaren da ta gindaya don ciyar da kasa da kuma al’umma gaba. Shi ya sa a wasu sassa na duniya za a tarar da jam’iyya daya ce ke godon mulki, ita kuma din da tsare-tsarenta da manufofinta da kuma hanyoyin aiwatar da su. Wata sa’a saboda kila rashin gudanar da al’amura yadda ya dace ko kuma saboda gajiya da tsohon tsarin da wannan jam’iyya take gabatarwa, sai a ga an samu jam’iyya mai adawa da wannan da ta yi dattin hula, ko kuma a samu wata da sauran jama’ar kasa ke ganin tsari da manufofinta sun fi wanda aka dade ana damawa da ita. Ta haka ne ake samun jam’iyya biyu ko uku suna tashe a cikin kasa domin a samar da zabi ga wadanda suka gaji da lamin wata siyasa.
Idan muka yi la’akari da irin wannan tsari sai mu ga cewa, ke nan idan an ga hayayyafar jam’iyyun siyasa a cikin tsarin gudanar da dimokuradiyya to ba wai alamun ci gaba ba ne, ni a tawa ai suna sane da wannan tunanin, amma suka takaita ko suka kasance sun zaba wa al’ummarsu jam’iyyu biyu, manya, masu gudanar da mulki domin jama’arsu. fahimta, alamun rarrabuwa ce da sukurkucewa da lalacewa. Wani na iya cewa amma ai tsarin dimokuradiyya ne ya bayar da wannan dama, domin tsari ne na gwamnatin jama’a don samar da ribar dimokuradiyya ga jama’ar. Amma idan muka natsu sosai za mu ga cewa kasashe kamar su Amurka da Rasha da Ingila da sauran irinsu, ai suna sane da wannan tunanin, amma suka takaita ko suka kasance sun zaba wa al’ummarsu jam’iyyu biyu, manya, masu gudanar da mulki domin jama’arsu. Duk da haka ba su bari komai ya tabarbare ko zuguguce ba. A tuna, ba zama suka yi suka ce lallai ilau jam’iyyu biyu za su kasance a cikin kasar ba, a’a, sun tabbatar da cewa ai dan Adam fuska biyu ce gare shi, ko dai mai ra’ayin rikau ko mai son kawo sauyi, ko da kuwa a cikin tsari na Kwaminisanci ne ko na Jari-Hujja. Koda kuma a cikin tsari ne na gargajiya ko na sarauta ko kuma na gado. Haka kuma koda a cikin tsari ne na addini, sai an samu irin wannan rarrabuwa. Saboda haka, biyu ta fi daya, ta kuma fi uku ko barkatai, in dai gaskiya ake bukata. Ke nan ana iya cewa Amurkawa ko Rashawa ko Biritaniyawa ko Larabawa ko Asiyawa da makantansu, sun yi haka, ni a tawa fahimta saboda sun yi amanna cewa dan Adam fasali biyu ke gare shi, wato ko dai wanda ake dannewa ko wadanda ke dannewa! In abubuwa sun yi kamari ne ake samun ’yan tsaka-tsaki ko ’yan ba-ruwanmu, wadanda su ba su amince da daya daga cikin wadannnan tsare-tsare ba.
Shi ya sa a Amurka tsarin siyasarta da dimokuradiyyarta ya kasance jam’iyyu biyu ne manya, su ne kuma ake ta fafatawa da su cikin fiye da tsawon shekara 200. Ko dai Jam’iyyar Democrats ko kuma Republicans, a kuma kula, ba wai haka nan wadannan jam’iyyu suka wanzu da karfin gwamnati ba, a’a tsari ne na gudanuwar al’umma a tsawon lokaci.