✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan a China

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaba Goodluck Jonathan ya sauka a birnin Beijing na kasar China domin fara ziyara a kasar inda ya…

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaba Goodluck Jonathan ya sauka a birnin Beijing na kasar China domin fara ziyara a kasar inda ya jagoranci wani babban ayari na jami’ai da ’yan kasuwar kasar nan. China ta bunkasa ta yadda ta zama daya daga cikin manyan abokan kasuwancin Najeriya. A lokacin ziyarar Najeriya da China za su sanya hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a fannonin da suka shafi harkar sufurin jiragen kasa da hanyoyi da man fetur da gas da nomad a tsaro kuma filayen jiragen sama. Alakar tattalin arziki tsakanin Najeriya da China tana ci gaba da bunkasa inda ta kai sama da Dala biliyan bakwai da miliyan 760 a shekara ta 2011 daga Dala miliyan 100 kacal a 1993.
China babbar kasa ce da ked a jama’ar da suka haura daukacin jama’ar Nahiyar Afirka, kuma ta bunkasa inda a zama ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya, ta wuce Japan kuma yanzu haka tana bin Amurka a gindi a gindi.
Akwai darussa da dama da Najeriya za ta koya daga China, daya daga cikin shi ne hanyar yaki da cin hanci da rashawa da almundahana – wato kashe manyan barayin gwamnati tare da kwace daukacin dukiyarsu. Na biyu kasancewar kowace kasa ana da ‘bukatuna na kasa,’ na kasar China a yanzu shi ne samar da dama ga mutanen China a gida da waje. Na uku wadatattun tsare-tsare da za su jawo ra’ayin masu zuba jari zuwa kasar China, wadanda ya wajaba Najeriya ta tsaya sosai ta nazarce su.
A lokacin ziyarar Shugaba Jonathan zai yi kokarin tabo batutuwan da suka shafi Najeriya. wadannan sun hada da cewa kayayyakin kasar China da ake sayarwa a Amurka da kasashen Turai suna da cikakken inganci, yayin da wadanda  ake sayarwa a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa suke marasa inganci. Bayanin da ake yawan yi shi ne ’yan kasuwar Najeriya da jami’an gwamnati ne suke neman kaya masu araha bai hujja b ace, domin hakan wata almundahana ne. Sannan mutanen China da suka bude kantunansu a na Najeriya ana yawan zarginsu da bautar da ma’aikata da wulakanta ma’aikatansu ’yan Najeriya.
Najeriya tana da ayyuka da ake gudanrwa da kudin kasar China, inda bankin China EdIM Bank ke ba da gagaarumar gudunmawa wajen gudanar da gine-gine. Kuma domin a kauce wa kantar bashi da aka fuskanta a baya, wajibi ne a bayyana ka’idojin komai a fili ta yadda Najeriya za ta iya shiga a dama da ita.
Kuma yayin da kamfanonin kasar China ke Najeriya wadanda ya kamata su dauki ma’aikata ’yan kasa, sai ya zamo wata dama da China za ta rika shigo da mutanenta tana samar musu da ayyukan yi. A harabobi da dama a wadannan kamfanonin za a iske mutanen kasar China na gudanar da ayyukan da suka kamata a ce ’yan Najeriya ne ke yi. Wajibi ne a shaida wa shugabannin kasar China balo-balo cewa ba za a lamunci hakan ba, domin manyan ayyukan gine-gine da ake gudanarwa su ne za su ba da dama ga kasar nan ta rage yawan matasa marasa aiki da take fama da su.
Dangantaka ko tattalin arziki ko siyasa tilas ne su gamsar da mafi karancin bukatun yarjejeniyar. Wajibi ne dangantaka da China ya ba Najeriya babbar dama na inganta kasuwanci da samar da ayyukan yi. Bai kamata Najeriya ta zama jujin kayayyakin kasar China ba, kamar yadda abin yake a yanzu. an ruwaito cewa mutanen China na kokarin kafa masana’antu a Najeriya, sai dai sun yi kadan bisa lura da girman kasuwa da yawan mutanen Najeriya. Don haka za su iya kafa manyan kamfanonin da za su rika sana’anta kayayyakin da suke bukata don aikin jiragen kasa da na lantarki da suke gudanarwa, bai kamata Najeriya ta kasance mai samar da albarkatun kasa kawai ba.
Lokacin da mutanen China suka gina hanyar jirgin kasa ta TAZARA a tsakanin Tanzaniya da Zambiya kimanin shekara 50 da suka gabata, ana gudanar da aiki ne da rana da dare a horar da ma’aikata ’yan Afirka, wannan ya sa lokacin da mutanen China suka tashi, ’yan Afirkan sun iya tafiyar da harkar jirgin kasan cikin nasara. Haka ya kamata a yi a yayin gudanar da aikin titin jirgin kasa na zamani daga Abuja zuwa Kaduna da kamfanin wutar lantarki na Zungeru da ayyuka filayen jiragen sama, a ba ’yan Najeriya damar koyon aikin kai-tsaye.
Ana yawan sukar fasahar kere-kere na China cewa bai dace da muhalli ba, bunkasar tattalin kasar China ga alama bai lura da muguwar illar da yake yi ga muhalli ba. Don haka wajibi ne jami’an Najeriya sun ace kan kamfanonin gine-gine na China sun kauce wa mafi karancin illar da suke ga muhalli.
Wakilan Najeriya a ziyarar su yi nazari a tsanake kan duk wata yarjejeniya da aka yi wa ado wajen tsarawa, kada su yi saurin amincewa da ita domin kada su fada tarkon kasar China.