✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Jonah Jang ne yake neman tunzura al’ummar Filato – Sale Bayari

A makon da ya gabata ne wadansu matasa suka je gidan gwamnatin jihar Filato da zauren majalisar dokoki ta jihar  da ke garin Jos, suna…

g Alhaji  Sale Bayari, Sakataren cigaban al’ummar FulaniA makon da ya gabata ne wadansu matasa suka je gidan gwamnatin jihar Filato da zauren majalisar dokoki ta jihar  da ke garin Jos, suna gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da matakin da gwamnan jihar Barista Simon Lalong  ya dauka na samar wa Fulani makiyaya wuraren kiwo a jihar.
Kafin  wannan zanga-zanga, tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta  Arewa  Jonah Jang, ya fito ya soki wannan kudiri na gwamna Lalong, wanda hakan ya jawo Gwamna Lalong   ya mayar masa da kakkausan martini, inda ya nuna cewa Jang ne ya fara kawo shawarar a yi haka a rahoton bincike na kwamitin Niki Tobi .
A tattaunawarsa da wakilinmu, Sakataren kungiyar cigaban al’ummar fulani ta Nijeriya [GAFDAN] Alhaji Sale Bayari ya yi bayanin cewa tsohon gwamnan Jonah Jang yana son ya sake  hassada rikici ne a jihar kan wannan al’amari. Kuma ya yi bayanin cewa al’ummar fulani suna da ‘yancin a ba su wuraren kiwo a jihar Filato.
Ya ce, ‘’tun a rikicin Jos na shekara ta 2001, aka ce ana son a samu  zaman lafiya tsakanin fulani makiyaya da manoma a wannan jiha ta Filato. To shi ne yanzu da aka zo ana neman hanyar da za a bi a samu zaman lafiyar, sai ga shi ta fito a fili cewa wadansu a jihar nan   ba sa son a samu wannan zaman lafiya. A cikin irin wadannan mutane   har da  tsohon gwamnan jihar nan kuma Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa  Jonah Jang, wanda yake   kan gaba wajen son sake haddasa fitina kan wannan magana ta samar wa fulani makiyaya wuraren kiwo a wannan jiha.Ya ce gwamnan jihar Filato na yanzu Barista Simon Lalong ya fito ne zai kwace gonakin manoma ya bai wa makiyaya.’’
‘’A samakon wadannan  maganganu da Jonah Jang ya yi kan wannan al’amari ya sanya a ranar litinin da talatar da ta gabata,  wadansu matasa suka je gidan gwamnatin jihar Filato da majalisar dokokin jihar Filato,  suka yi zanga-zangar nuna cewa su ba su yarda  a bai wa Fulani makiyaya wurare kiwo a jihar Filato ba.’’
‘’To, ni ban manta da abin da Jonah Jang ya yi ba a shekara ta 2009, lokacin da yake gwamnan jihar nan, ya je  ya sa aka yi amfani da manyan motoci a yankin bashar a karamar hukumar Wase. Aka kwashe al’ummar Fulani makiyaya da karfin tsiya, matansu da kananan yara, aka je aka zubar  da su a wadansu wurare a jihohin Bauchi da Gombe.  Ya ce wai daga wadannan jihohi suka zo wannan jiha ta Filato.’’
‘’Don haka mun riga mun san cewa a lokacin mulkin Jonah Jang ya haddasa fitina da  kashe-kashe da gaba a tsakanin al’ummar jihar Filato. Kuma ga shi har yanzu bai gaji ba.Wannan abin bakin ciki ne kwarai da gaske. Yau abu ya fito fili cewa Jonah Jang  tare da al’ummarsa ne ba sa son a zauna lafiya a jihar Filato. Domin gwamna Lalong ya fito don  tabbatar da wannan shiri na bai wa fulani makiyaya wuraren kiwo a jihar nan,  ga shi Jonah Jang ya fito ya ce kada a yarda, domin  Simon Lalong saboda siyasa yana son ya kwace gonakin manoma  ya bai wa fulani  makiyaya baki.’’
Ya kamata Jonah Jang da jama’arsa su tuna a lokacin da aka yi  rikicin Jos na shekara ta 2001 an kafa hukumar binciken wannan rikici karkashin mai shari’a Nikki Tobi. Ni kaina na wakilci al’ummar Fulani a  wannan hukuma. A lokacin da wannan hukuma take wannan aiki na binciken abin da ya kawo wannan rikici. An yi maganar cewa mene ne yasa  wannan rikici na Jos ya yadu zuwa kananan hukumomin  Jos ta kudu da Barikin Ladi da Riyom da Bassa. A lokacin sai manoman wadannan yankuna suka ce abin da ya kawo wannan rikici a wadannan yankuna, shi ne shekara da shekaru fulani suna yi masu ta’adi a gonakinsu. Don haka suka kawo shawarar a bai wa fulani wuraren da za su rika yin kiwo, don su daina shiga masu gonaki.  Don haka shugaban wannan hukuma mai shari’a Nikki Tobi ya yarda da wannan shawara, don haka a  rahoton kwamitin.  Ya kawo shawarar gwamnati ta yi makiyaya a Barikin Ladi da Riyom da Jos ta kudu da Bassa  da sauran kananan hukumomin jihar Filato .’’
‘’A lokacin  tsohon gwamnan jihar nan  Cif Joshua Dariye ne yake gwamnan jihar, har ya gama mulkinsa bai iya aiwatar da rahoton wannan kwamiti ba. Bayan  da Jonah Jang ya zo  a shekara ta 2007, da hawansa sai ya fitar da matsayin gwamnati (White paper)  kan rahoton wannan kwamiti. Ya ce zai aiwatar da rahoton wannan kwamiti don a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan. Ya ce shawarar da wannan kwamiti ya bayar kan samar wa makiyaya wuraren kiwo za a yi, amma  a karshe sai yaki ya aiwatar da wannan al’amari.Yanzu kuma  da ya duba ya ga cewa gwamna Simon Lalong zai yi, sai ya je yana neman wadanda za su yi zanga-zangar da za ta   jawo rikici a jihar Filato.’’