Shugaban Amurka, Joe Biden, ya sa hannu kan wata doka ta ke bayar da dama ga matan da ke son zubar da ciki.
Sabuwar dokar yanzu ta ba mata tsallakawa daga wata jihar zuwa wata domin a zubar musu da ciki.
- Gwamnatin Filato ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar
- Ba mu da wani shafin Hausa in ba na Aminiya ba – Daily Trust
Shugaba Joe Biden ya sa wa dokar hannu ne ranar Laraba sai na ta faman kokari warware wani tarnaki da dokar ke fuskanta.
Tarnakin kuwa shine ta ci karo da wata dokar da ta haramta a yi amfani da kudin gwamnati don a biya a zubar da ciki, sai dai idan rayuwar mai cikin na cikin hatsari, ko ta samu cikin ne ta hanyar fyade ne, ko saduwa da muharraminta.
Kakakin Fadar White House, Karine Jean-Pierre ta ce, hukumar kula da lafiya za ta gayyaci jihohin da zubar da ciki ba laifi bane, da su nemi izinin amfani da kudaden da aka ware na taimakon lafiya don su samar da kula da lafiyar matan da ke zaune a jihohin da aka hana zubar da ciki.
Wata kungiya mai goyon bayan zubar da ciki ta ce ta samu karuwar mata da yawa da ke bukatar taimakon zuwa wani wuri don a zubar musu da ciki.
Kungiyar ta ce ta biya dakunan kwana 76 da biyan kudina motocin haya, kama kujera a jirgi ko kotar safa na tafiye-tafiye sau 52. Kari a kan irin wannnan bukata a a shekarara ta wuce.