✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin yakin Rasha ya yi taho-mu-gama da na Amurka a sararin samaniya

Amurka ta zargi Rasha da kokarin kakkabo jirgin nata mara matuki

Wani jirgin yaki mallakin kasar Rasha ya yi taho-mu-gama da jirgin Amurka mara matuki a sararin samaniya, saman tekun Black Sea.

A cewar Rundunar Sojin Amurka a cikin wata sanarwar da yammacin Talata, lamarin dai ya tilasa mata saukar da jirgin nata cikin gaggawa.

Ta ce jirgin nata na kan shawagi ne a sararin samaniyar kasa da kasa, lokacin da jiragen yakin Rasha biyu suka yi yunkurin kakkabo shi.

Rundunar ta Amurka mai kula da kasashen Turai ta ce lamarin ya faru ne sakamakon gangancin Rasha.

Sai dai sanarwar ta ce Amurka za ta ci gaba da shawagin duk da barazanar.

“Jirginmu kirar MQ-9 na gabatar da shawaginsa a sararin samaniya lokacin da jiragen yakin Rasha suka yi yunkurin kai masa hari, lamarin da ya tilasta taho-mu-gama tare da kwace wa matukansa,” a cewar Shugaban Rundunar Sojin Saman Amurka, Janar James Hecker.