Wani jirgin yaki, samfurin Hawk T1 mallakin Rundunar Sojin Ruwa ta kasar Birtaniya ya yi hatsari a safiyar Alhamsi a yankin Cornwall.
Ma’aikatar Tsaron Birtaniya ta tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin yakin na rundajar ta 736 daga RNAS Culdrose a lardin Lizard peninsula, sai dai babu wanda ya mutu.
- An yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami, Sheikh Al-Sabuni
- Gobara ta babbake unguwar marasa galihu a Saliyo
- An kama matar da ta kashe kishiyarta ta kona gawar
“Matukan jirgin su biyu na samun kulawa daga jami’an lafiyar bayan sun yi saukar lema daga jirgin yakin. A halin yanzu ba za mu bayar da karin bayani ba,” inji Ma’aikatar tsaron.
Asibitin Cornwall ya wallafa a shafinsa cewa, “An dauki mutanen su biyu a wani jirgi zuwa Asibitin Derriford inda za a yi jinyar raunukan da suka samu… Har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da aiki a wurin da abin ya faru.”
Kamfanin mai jiragen daukar marasa lafiya ya ce, ya kai dauki ne bayan samu rahoton lalacewar “injin jirgin saman” a yankin Helston, kuma mutane biyu da ke ciki sun samu raununa.