Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya bace yayin taimaka wa rundunar sojan Najeriya ta Bataliya 145 a garin Damasak Arewacin Borno.
Kamar yadda mai magana da yawun sojin kasar Ibikunle Daramola ya sanar da cewa, jirgin mai saukar ungulu ya na taimakawa dakarun sojin kasa ne da ke yaki da ‘yan Boko Haram a garin Damasak da ke jihar Borno da maraicen jiya Laraba.